Bankin BOI Ya Ƙaddamar da Shirin Ba da Rancen Naira Biliyan 2 ga ’Yan NYSC

Bankin BOI Ya Ƙaddamar da Shirin Ba da Rancen Naira Biliyan 2 ga ’Yan NYSC

  • Bankin Masana’antu na Najeriya ya ware naira biliyan 2 domin bai wa ’yan bautar ƙasa rance har naira miliyan 5 kowanne
  • Za a karɓi rancen da kuɗin ruwa 9% a shekara, tare da biyan sa cikin shekaru uku kamar yadda shirin ya alanta kwanan nan
  • Masu neman rancen dole ne su kasance ’yan NYSC masu ingantaccen tsarin kasuwanci da bankin ya gamsu zai haifar da da mai ido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Bankin Masana’antu (BOI), tare da haɗin gwiwar Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), ya ƙaddamar da shirin bayar da rancen naira biliyan 2 ga matasan da ke bautar ƙasa domin su fara kasuwanci ko faɗaɗa wanda suke da shi.

A ƙarƙashin shirin, wanda ya cancanta zai iya karɓar rance har naira miliyan 5 domin kafa sana’a ko bunƙasa ƙaramar sana’ar da yake gudanarwa.

Idan baku manta ba, ana kuka a Najeriya kan rashin sana'ar matasa, musamman wadanda suka kammala karatu a jami'o'i a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

Rancen 'yan NYSC daga BOI
Bashin da za a bai wa matasa masu NYSC | Hoto: boi.gov.ng/fmino.gov.ng
Source: UGC

Sharuɗɗan karɓar rancen

Bankin ya bayyana cewa za a karɓi rancen ne da kuɗin ruwa na 9% a duk shekara, sannan masu cin gajiyar shirin za su biya bashin cikin shekaru uku.

Haka kuma, bankin ya bayar da wa'adin watanni uku kafin fara biyan rancen da kuɗin ruwa. Wannan lokacin zai ba wa masu cin gajiyar damar kafa kasuwancinsu kafin fara biyan bashin.

BOI ya jaddada cewa tallafin rance ne ba kyauta ba. Saboda haka, amincewa da buƙatar mutum zai dogara ne kan ingancin tsarin kasuwancinsa da kuma yiwuwar samun riba.

Waɗanda suka cancanta

Shirin ya shafi ƙananan sana’o’i da za su iya samar da kuɗin shiga tare da samar da guraben ayyukan yi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Masu neman rancen dole ne su kasance ’yan bautar ƙasa a halin yanzu, kuma suna da ingantaccen tunanin kasuwanci ko kuma suna gudanar da ƙaramar sana’a.

Bankin ya lissafa wasu fannoni da za su iya amfana da shirin, ciki har da:

Kara karanta wannan

Mutane suna shan wahala a kasa, Tinubu ya shirya kawo sauki ta hanyar sufuri

  • Noma
  • Sana’ar ɗinki da ƙera tufafi
  • Fasaha
  • Sarrafa kayan abinci
  • Kula da harkokin girki da abinci
  • Ayyukan intanet
  • Ƙananan masana'antu

Dole ne tsarin kasuwancin mai nema ya nuna cewa sana’ar na da damar samun riba da kuma ɗorewa.

Yadda ake neman rancen

’Yan bautar ƙasar da ke son neman rancen za su yi rajista ta shafin NYSC Skills Acquisition and Entrepreneurship Development (SAED).

Matakan neman sun haɗa da shiga shafin NYSC na hukuma, zuwa sashen SAED, sannan shirya cikakken tsarin kasuwanci da hasashen kuɗaɗen shiga da kashewa.

Ana kuma buƙatar masu neman rancen su tuntuɓi jami’an SAED na NYSC domin samun bayanai kan lokacin karɓar buƙatu da ranar tantance masu nema.

Kammala horon koyon sana'a da kuma tantancewar BOI na daga cikin sharuɗɗan da ake buƙata kafin bankin ya yanke shawarar bayar da rancen.

Babu sabon wa'adin nema

Ko da yake an ƙaddamar da shirin ne a watan Oktoban 2025, BOI bai sanar da sabon wa'adin neman rancen ko wata hanyar tura buƙatu da ke aiki a yanzu ba.

Kara karanta wannan

An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Saboda haka, ana shawartar masu sha'awar neman rancen da su tabbatar da halin da shirin yake ciki ta shafin ayyukan tallafin BOI ko kuma jami'an SAED na NYSC.

Bankin ya kuma bayyana cewa yin rajista a shirin SAED ko aika tsarin kasuwanci ba ya nufin an tabbatar wa mutum da samun rancen. Za a tantance kowace buƙata bisa ƙarfin kasuwancin da yadda mai nema zai iya biyan bashin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng