Sheikh Ahmad Gumi Ya Fitar da Sako kan Kisan da Aka Yi Wa Masussuka a Katsina

Sheikh Ahmad Gumi Ya Fitar da Sako kan Kisan da Aka Yi Wa Masussuka a Katsina

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a matsayin babban kuskure da ka iya jawo fitina a cikin al’umma
  • Malamin ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar maƙiyan Musulunci su yi amfani da lamarin wajen haifar da ruɗani
  • Gumi ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su bar hukuma ta ɗauki matakin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria — Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bukaci al'umma su bar hukumomin tsaro su yi aikinsu kan kisa Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka

Babban malamin mazaunin Kaduna ya bayyana kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a matsayin babban kuskure da ka iya haifar da fitina a cikin al’umma.

Ahmad Gumi.
Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Source: Facebook

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da barin hukumomin da abin ya shafa su gudanar da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Kara karanta wannan

Kungiyar Amnesty ta shiga batun kisan Sheikh Masussuka a Katsina

A cikin saƙon, malamin ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar amfani da kisan wajen haifar da ruɗani a tsakanin al’umma, yana mai cewa maƙiyan addinin Musulunci na iya amfani da irin wannan lamari domin tayar da fitina.

Abin da Gumi ya ce kan kisan

A cikin saƙon nasa, Sheikh Gumi ya yi nuni da ayar Alƙur’ani da ke cikin Suratun Nur, aya ta 63, wadda ke gargaɗin waɗanda suke saɓa wa umurnin Allah kan yiwuwar fuskantar fitina ko azaba mai raɗaɗi.

Malamin ya kuma kawo Suratun Nisa’i, aya ta 83, wadda ta yi magana kan yadda ya kamata a mayar da al’amuran tsaro da na fargaba ga Manzo da masu ruwa da tsaki domin su tantance su yadda ya dace.

Ya yi amfani da ayoyin ne wajen jaddada muhimmancin kauce wa abin da zai iya haddasa fitina, tare da yin taka-tsantsan wajen yaɗa bayanan da ka iya tayar da hankulan jama’a.

Kara karanta wannan

Farfesa Makari ya yi magana kan kashe Sheikh Masussuka

Ya yi addu’ar zaman lafiya

Sheikh Gumi ya kammala saƙonsa da addu’ar Allah Ya ba al’ummar Musulmi zaman lafiya, tare da kawar da duk wata fitina daga al’ummar Annabi Muhammad (SAW).

Kiran na zuwa ne bayan da rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da abokinsa, Adamu Abubakar.

Mutanen biyu sun rasu ne sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai musu a gaban gidan malamin da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma a ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Masussuka.
Babban malamin musulunci a Najeriya, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka
Source: Facebook

A cewar sanarwar rundunar ’yan sandan, maharan biyu da ke kan babur sun buɗe wa mutanen wuta da misalin ƙarfe 7:30 na dare, inda suka raunata su har lahira.

Rundunar ta ce ta fara bincike kan lamarin, tare da tura jami’an tsaro na musamman domin taimakawa wajen cafke waɗanda ake zargin.

Gwamnan Katsina ya yi magana

Kun ji cewa Gwamna Dikko Radda ya bayyana alhininsa kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka, fitaccen malamin addinin Musulunci mai wa’azin zaman lafiya.

Radda ya ce gwamnati za ta tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano wadanda suka aikata kisan da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262