Abin da Aka Gani a Jikin Gawar Sheikh Yahaya Masussuka bayan Kai Ta Asibiti a Katsina
- Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina ya tabbatar da cewa ba a gudanar da binciken gawa kan Sheikh Yahaya Masussuka ba bayan kashe shi
- An yi wa gawarsa tanadin da ake yi wa gawa kafin jana’iza, kuma har yanzu tana a dakin ajiye gawa gabanin jana’izarsa da aka shirya ranar Juma’a, 30 ga Oktoba
- Wani jami'in asibitin ya tabbatar da cewa ya ga raunuka a jikin gawar, amma ya ƙi bayyana abin da ya haddasa su ba tare da an gudanar da bincike ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina ya tabbatar a ranar Alhamis cewa ba a gudanar da binciken gawa kan gawar malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka ba.
Asibitin ya bayyana cewa babu wani gwajin gawa da aka yi wa Sheikh Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga suka kashe tare da wani abokinsa a Dutsin-Ma kwanaki uku da suka gabata.

Source: Facebook
Premium Times ta ruwaito cewa an yi wa gawar tanadin da ake yi wa gawa kafin a binne ta, kuma har yanzu tana a dakin ajiye gawarwaki na asibitin gabanin jana’izar da aka shirya yi ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.
Abin da asibitin ya bayyana
Yahaya Yahuza, ma’aikacin da ke kula da sashen ajiye gawarwaki na asibitin, ya shaida wa Premium Times yayin ziyarar da suka kai asibitin ranar Alhamis cewa an kawo gawar Malam Masussuka da misalin ƙarfe 2:20 na dare ranar Talata.
Ya ce ’yan uwansa ne suka kawo gawar, kuma malamin ya riga ya rasu kafin isowarsa asibitin.
“Ba a yi masa binciken gawa ba. Abin da aka yi kawai shi ne tanadin gawar kafin jana’iza,” in ji Yahuza.
Ya tabbatar da cewa har yanzu gawar tana asibitin a ranar Alhamis, kuma ’yan uwan mamacin sun sanar da jami’an asibitin cewa suna shirin karɓarta da safiyar Juma’a.
Da aka tambaye shi dalilin jinkirta jana’izar, Yahuza ya ce bai sani ba.
“Ba ni da masaniya kan wannan, domin ’yan uwansa ne suka san dalilin da ya sa suka bar gawar a nan har zuwa wannan lokaci,” in ji shi.
An ga raunuka a gawar Masussuka
Jami'in asibitin ya kuma tabbatar da cewa ya ga raunuka a jikin gawar, amma ya ƙi bayyana abin da ya haddasa su ba tare da an gudanar da binciken likitanci ba.
“Akwai raunuka a jikinsa. Amma likitoci ne za su tabbatar da ainihin abin da ya faru da shi,” in ji Yahaya Yahuza.

Source: Facebook
Matakin da Bola Tinubu ya dauka
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa, Adamu Abubakar
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan malamin da abokinsa, tare da cafke waɗanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kotu.
Asali: Legit.ng

