Obasanjo Ya Sake Taso Bola Tinubu a Gaba, Ya Fadi Shirmen da Ya Yi

Obasanjo Ya Sake Taso Bola Tinubu a Gaba, Ya Fadi Shirmen da Ya Yi

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya soki Bola Tinubu kan cewa karbo bashi ba cutar kuturta ba ce, yana mai cewa maganar banza ce
  • Obasanjo ya ce bashin da ake karbowa ya fi kuturta muni, domin kuturta na hallaka mutum guda, amma bashi yana lalata rayuwar tsararraki
  • Ya kuma tambayi dalilin da ya sa darajar Naira ta fadi matuka cikin shekaru 47, tare da sukar dogaro da Bankin Duniya da IMF

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan salon mulkin da yake yi.

Obasanjo ya dura kan Tinubu bisa kalamansa cewa karbo bashi ba cutar kuturta ba ce, yana mai cewa wannan maganar banza ce.

Obasanjo ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a a Abeokuta, Ogun, yayin wani taron dandalin Ajibosin mai taken amfani da fasahar basirar na’ura wajen magance matsalolin al’umma da bunkasa kasa, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Magana ta fara fitowa, an ji dalilin da ya sa Tinubu ke son karbo bashin kusan Naira tiriliyan 30

A watan Afrilu, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karbo bashi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, yana mai cewa bai kamata a dauke shi a matsayin wani abu mara kyau ba.

Shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a Fadar Shugaban Kasa yayin ganawa da wasu shugabannin Plateau karkashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Nentawe Yilwatda.

Tinubu ya ce:

“Idan ya zama dole mu karbo bashi, za mu karbo. Karbo bashi ba kuturta ba ce, kawai muna bukatar mu yi aiki tukuru domin mu iya biya.”

Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke nuna damuwa kan karuwar bashin kasar da kuma yawan kudaden shiga da ake kashewa wajen biyan basussukan.

Da yake mayar da martani, Obasanjo ya yi kakkausar suka ga Tinubu, yana mai cewa kuturta tana iya lalata mutum daya a lokaci guda, amma bashi yana lalata tsarurrukia.

Tsohon shugaban kasar ya ce: “Duk wanda ya ce bashi ba kuturta ba ne, to maganar banza ce tsantsa. Bashi ya fi kuturta muni. Domin kuturta mutum daya take lalatawa, amma bashi yana lalata tsararraki.”

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Bafarawa ya kafa sharadin yi wa Tinubu kamfen a 2027

Obasanjo ya koka kan faduwar darajar Naira

Obasanjo ya kuma nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da tattalin arzikin Najeriya, inda ya tuna cewa lokacin da ya fara gonarsa shekaru 47 da suka wuce, Naira ta fi karfin dala.

Ya ce:

“Lokacin da na fara gonata shekaru 47 da suka wuce, Naira daya tana canjawa da dala $1.85. Shekaru 47 kenan. Me Najeriya ta yi a cikin wadannan shekaru 47 har muka kai Naira 1,500 kan dala daya? Me muka yi?”

Ya kuma tambayi ko shugabannin siyasar kasar suna da kwarewar yanke shawarar da za ta inganta rayuwar ‘yan Najeriya da kuma magance matsalolinsu.

Obasanjo ya tambaya: “Me shugabanninmu suka sani? Kuma me ba su sani ba? Daga cikin abubuwan da suka sani, me za su iya yi mana?”

Ya soki dogaro da Bankin Duniya da IMF

Tsohon shugaban kasar ya kuma soki yadda Najeriya ke dogaro da cibiyoyin kasashen waje, musamman Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF).

Kara karanta wannan

Taohon shugaban APC na Kano ya gamu da hatsari a hanyar dawowa daga wurin kamfen Tinubu

Ya ce manufofin cibiyoyin ba lallai ne su dace da yanayin Najeriya da irin matsalolin tattalin arzikinta ba.

Obasanjo ya tuna yadda aka hana Najeriya tallafa wa noma, duk da cewa kasashen da suka ci gaba suna ba manoma tallafi mai yawa.

Ya ce:

“Ba don mu aka kafa Bankin Duniya da IMF ba. Ba mu ne muka gina su ba. An kafa su kafin mu samu ‘yancin kai. Amma su ne za su rika gaya mana abin da za mu yi.”

Obasanjo ya kuma yi gargadin cewa bai kamata Najeriya ta rika bin shawarwarin tattalin arziki na kwararrun da suka yi karatu a kasashen waje ba tare da la’akari da hakikanin yanayin kasar ba.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.