Shugaba Bola Tinubu Ya Dura a Kaduna domin Kaddamar da Yakin Neman Zaben APC
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Jihar Kaduna domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC gabanin babban zaɓen 2027
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, da Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ne suka tarbi mai girma shugaban ƙasar yau Asabar, 24 ga Oktoba, 2026
- Dubban magoya bayan jam'iyyar APC, ministoci, gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na tarayya da na jihohi sun hallara a wurin taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Jihar Kaduna domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a hukumance gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
An tsara kaddamar da yakin neman sake zaben Tinubu/Shettima a yau Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2026.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ne suka tarbi shugaban ƙasar kafin fara gangamin yaƙin neman zaɓen.
Dubban magoya bayan APC, tare da ministoci, gwamnoni, ’yan majalisa da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar, sun hallara a wurin taron domin halartar bikin ƙaddamar da kamfen ɗin.
Wannan gangami ya nuna fara yaƙin neman zaɓen jam’iyyar mai mulki a hukumance, yayin da take ƙoƙarin ganin Tinubu ya sake samun wa’adin mulki na biyu.
Zaɓin Kaduna a matsayin wurin ƙaddamar da kamfen ɗin na bai wa APC wata muhimmiyar dama ta tattara goyon baya a Arewacin Najeriya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai iya zuwa kowace jiha a Najeriya domin halartar taron yakin neman zabe ba saboda ayyukan gwamnati sun masa yawa.
Wannan mataki da Tinubu ya dauka ya ja hankalin yan Najeriya musamman wadanda ke jam'iyyun adawa, inda suka fara hasashen abubuwa da dama da suka sa shugaban kasa ba zai je kowace jiha ba
Sai dai kwamitin kamfen APC ya fitar da tsare-tsaren gangami a jihohin Najeriya, yana mai nuna cewa Tinubu zai halarci jihohi 12 ne kacal.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Jami'an tsaro sun mamaye wuraren da aka liƙa fastoci da allunan tallata Tinubu
Daga cikin wadannan jihohi akwai Kaduna, daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma, inda aka tsara kaddamar da kamfen APC hukumance ranar Asabar, 24 ga watan Oktoba, 2026.
Shugaba Bola Tinubu ne zai jagoranci kaddamar da yakin neman zabensa karo na biyu kuma rahotanni sun tabbatar da cewa yanzu haka yana cikin birnin Kaduna.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
