Tinubu Zai Fara Karɓar Harajin 25% daga Kuɗaɗen Shigan Ƴan Najeriya?
- Sanata Ireti Kingibe ta yi ikirarin cewa sabbin dokokin haraji sun tilasta wa ’yan Najeriya biyan harajin kashi 25 cikin 100 na kuɗin shigarsu
- Bincike ya nuna cewa ikirarin ba gaskiya ba ne, domin dokar ta tanadi tsarin haraji bisa matakan kuɗin shiga da mutum yake samu
- Dokar haraji ta tanadi kashi 25 cikin 100 ne kawai ga kuɗin shigar shekara da ya haura naira miliyan 50, kuma ta fara aiki tun Janairu 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sanata Ireti Kingibe, mai wakiltar Abuja, ta yi ikirarin cewa sababbin dokokin haraji sun wajabta wa kowane ɗan Najeriya biyan harajin kashi 25 cikin 100 na kuɗin shigarsa.
Ta ƙara da cewa gwamnati ba ta fara aiwatar da wannan tanadi ba saboda tsoron fuskantar suka daga ’yan Najeriya.

Source: Twitter
Zargin Sanata Kingibe kan Tinubu
Misis Kingibe, mamba a jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC), ta yi wannan ikirari ne yayin da take jawabi ga magoya bayanta a wani taro a Abuja, cewar Punch.
Ba a iya tabbatar da ranar gudanar da taron da kansa ba, amma wani bidiyon jawabinta da ta gabatar da harshen Pidgin ya bazu sosai a kafafen sada zumunta.
Ta bukaci magoya bayanta su kada kuri’a kan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a dukkan matakai, tana mai cewa manufofin gwamnati sun ƙara tsananta wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ta ce:
“Ƙasarmu ce wannan, kuma dole ne mu karɓe ta. Ba su ne za su yi mana ba. Mu ne za mu yi hakan. Idan ba mu gamsu da halin da ƙasar take ciki ba, mu ne za mu sauya ta. Babu wani da zai yi mana hakan. Dole ne mu tashi tsaye mu ce mun gaji. Mun sha wahala sosai.
"Ta yaya kuke tsammanin mutane za su iya rayuwa? Kun ƙara kuɗin wutar lantarki, amma me kuka yi da kuɗin? Babu komai. Yanzu kuna son ƙara haraji zuwa kashi 25 cikin 100 na duk abin da mutane suke samu, alhali kuɗin da suke samu yanzu ma bai isa biyan bukatunsu ba.
“Duk waɗannan abubuwan da na faɗa muku, Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta riga ta mayar da su doka. Tsoro ne kawai ya hana su fara aiwatar da su."
Binciken gaskiyar ikirarin Sanata Kingibe
Domin tantance gaskiyar ikirarin, Premium Times ta binciki dokar harajin Najeriya ta shekarar 2025, musamman sashe na 58, wanda ya yi bayani kan matakan harajin kuɗin shiga da ya shafi mutane.
Dokar ta tanadi keɓance mutanen da suke samun mafi ƙarancin albashi na ƙasa daga matakan harajin da aka bayyana a jadawalin dokar.
Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta zartar da dokar harajin Najeriya da wasu dokokin garambawul ga haraji guda uku a watan Yunin 2025.
An wallafa su a cikin kundin dokokin gwamnati a watan Satumban 2025, kuma sun fara aiki a ranar 1 ga Janairun 2026.
Sashe na 58 ya bayyana cewa harajin da mutum zai biya kan kuɗin shigarsa da ake iya harajinsa a kowace shekarar tantance haraji zai kasance bisa yadda aka tsara a jadawali na huɗu na dokar.
Sai dai wannan tanadi bai wajabta biyan harajin kashi 25 cikin 100 ga dukkan ’yan Najeriya a kan duk kuɗin shigarsu ba.
Maimakon haka, yana nuni ne da matakan haraji daban-daban da aka tsara a jadawali na huɗu, waɗanda ake amfani da su wajen lissafa harajin kuɗin shiga da ya cancanci a biya.
Matakan haraji da dokar ta tanada
A ƙarƙashin jadawalin dokar, ba a karɓar haraji kan naira 800,000 na farko daga kuɗin shigar shekara da ya cancanci haraji.
Ana karɓar harajin kashi 15 cikin 100 kan naira miliyan 2.2 na gaba, sannan kashi 18 cikin 100 kan naira miliyan 9 na gaba.
Haka kuma, ana karɓar kashi 21 cikin 100 kan naira miliyan 13 na gaba, yayin da naira miliyan 25 na gaba ke fuskantar harajin kashi 23 cikin 100.
Duk kuɗin shigar da ya haura naira miliyan 50 a shekara yana fuskantar harajin kashi 25 cikin 100.
Saboda haka, kashi 25 cikin 100 shi ne mafi girman matakin harajin kuɗin shiga na mutum, ba wai harajin da ake karɓa kai tsaye daga duk kuɗin shigar kowane ɗan Najeriya ba.
Yan bindiga sun kakabawa manoma haraji
An ji cewa 'yan bindiga a jihar Benue sun nemi wani manomi da ya biya su kuɗi N500,000 kafin ya sami damar shiga gonarsa domin girbe amfani.
Matakin na zuwa ne a yayin da 'yan bindiga ke ci gaba da addabar mutanen ƙauyen Mbagena da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala tare da daurawa manoma haraji.
Dan manomin, John James, shi ne ya tonawa 'yan bindigar asiri yayin wani taron bita da kungiyar SERAP ta shirya a garin Makurdi.
Asali: Legit.ng



