Jiragen Kasa 2 Sun Yi Tabo Mu Gama Suna tsakiyar Tafiya, Mutane da Dama Sun Mutu

Jiragen Kasa 2 Sun Yi Tabo Mu Gama Suna tsakiyar Tafiya, Mutane da Dama Sun Mutu

  • Aƙalla mutane 39 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan jiragen ƙasa biyu masu saurin gaske sun yi karo a Spain
  • Jiragen sun yi karo ne a layin dogo na Madrid zuwa Andalusia, inda wasu turakun jiragen suka kauce daga kan layin dogo suka gangara ƙasa
  • Firaministan Spain, Pedro Sanchez, ya bayyana alhininsa kan lamarin, yayin da jami’an agajin gaggawa ke ci gaba da aikin ceto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Spain - Aƙalla mutane 39 sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan jiragen ƙasa biyu da ke tsala gudu sun yi karo a Spain.

Hatsarin ya faru ne a layin dogo da ya haɗa birnin Madrid da yankin Andalusia, tsakanin garuruwan Los Yébenes da Urda da ke lardin Toledo.

Jiragen kasa.
Wurin da jiragen kasa suka yi karo a kasar Spain Hoto: Javier SORIANO
Source: Getty Images

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa jami’an agajin gaggawa suna ci gaba da aikin ceto waɗanda suka tsira da kuma neman mutanen da ka iya kasancewa a makale a cikin tarkacen jiragen.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa

Akalla mutane 39 sun mutu

Hukumomin yankin sun shaida wa Al-Jazeera cewa aƙalla mutane 39 sun mutu, duk da cewa ba a tabbatar da cikakken adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata ba.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin ƙasa mai saurin gaske na Renfe AVE ya tashi daga Madrid da ƙarfe 8:00 na safe zuwa Seville lokacin da ya yi karo da wani jirgin Iryo da ke tafiya a hanyar da ba tashi ba.

Ana zargin jiragen biyu suna ɗauke da fasinjoji sama da 400. Hotunan da aka ɗauka a wurin da hatsarin ya faru sun nuna turakun suka tarwatse.

An ga wasu fasinjojin suna ƙoƙarin tsira da rayukansu, yayin da ake zargin wasu mutane sun makale a cikin tarkacen jiragen.

A halin da ake ciki, jama’a sun taru a tashar jirgin ƙasa ta Atocha da ke Madrid domin neman bayanai kan ’yan uwansu da ke cikin jiragen lokacin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake auka wa Kaduna, sun kuma yin garkuwa da bayin Allah

Firaministan Spain ya yi alhini

Firaministan Spain, Pedro Sanchez, ya ce ya girgiza matuƙa da faruwar hatsarin, tare da bayyana goyon bayansa ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu.

Pedro Sanchez
Firaministan kasar Spain da ke nahiyar Turai, Pedro Sanchez Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce:

“Jami’an agajin gaggawa suna aiki a wurin domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa da kuma tabbatar da tsaronsu, tare da haɗin gwiwar dukkan hukumomin da abin ya shafa.
“Ina miƙa ta’aziyya ta, goyon baya da kuma jaje ga dukkan waɗanda abin ya shafa da iyalansu.”

Jirgin kasa ya kade mota a Legas

A wani labarin, kun ji cewa wani direba mai shekaru 55 ya tsallake rijiya da baya bayan jirgin ƙasa ya buge motarsa kirar Honda a layin dogo ta PWD da ke jihar Legas.

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa hatsarin ya haɗa da jirgin ƙasa da ke tafiya zuwa Agege da kuma motar Honda mai lambar rajista EKY 902 JT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262