Ana Son Ba da Diyyar N1.4bn ga Iyalan Masu Hakar Ma'adinan da Aka Kashe a Neja

Ana Son Ba da Diyyar N1.4bn ga Iyalan Masu Hakar Ma'adinan da Aka Kashe a Neja

  • Kwamitin gwamnatin tarayya ya bukaci a gurfanar da manyan jami’an NSCDC da ake zargi da hannu a mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a Minna
  • Kwamitin ya kuma ba da shawarar biyan Naira biliyan 1.4 ga iyalan mutum 33 da suka mutu da kuma mutum 44 da suka tsira
  • Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin kwamitin domin tabbatar da an yi adalci ga waɗanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kwamitin da ya binciki mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a hannun hukumar tsaro ta NSCDC a Minna, jihar Neja, ya ba da shawarar sallamar manyan jami’an da ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

Shugaban kwamitin mai mambobi 10, Jonathan Kure, ne ya bayyana hakan ranar Talata lokacin da ya miƙa rahoton binciken ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a Abuja.

Kwamitin binciken NSCDC
Mutanen da aka nada su yi bincike kan kisan masu hakar ma'adinai. Hoto: Federal Ministry of Interior
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Kure ya ce kwamitin ya gano cewa za a iya kaucewa mutuwar mutanen, yana mai cewa an tsare waɗanda abin ya shafa, ciki har da ƙananan yara 14, a yanayi na rashin mutunta mutunci da haƙƙin ɗan Adam.

An bukaci a sallami kwamandan NSCDC

Kwamitin ya ba da shawarar sallamar kwamandan hukumar NSCDC na jihar Neja nan take, tare da sauran jami’an da suka taka rawa kai tsaye wajen tsare masu haƙar ma’adinan da mutuwarsu daga bisani.

Ya kuma bukaci a gurfanar da jami’an da aka samu da hannu a lamarin domin a tabbatar da adalci.

Baya ga hukunta jami’an, kwamitin ya ba da shawarar yin gyare-gyare a cikin hukumar NSCDC domin inganta shugabanci da hana sake faruwar irin wannan lamari.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare, masu bincike sun gano abin da ya yi sanadin mutuwar matasa 37 a ofishin NSCDC

Za a biya diyyar N1.4bn

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa an ba da shawarar biyan jimillar Naira biliyan 1.4 a matsayin diyya ga iyalan mutum 33 da suka mutu da kuma mutum 44 da suka tsira.

Ya jaddada cewa mutuwar waɗanda aka tsare za a iya kauce mata idan da an kula da yanayin da aka ajiye su.

A cewar rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa kwamitin ya gano cewa mutanen sun mutu ne sakamakon rashin isasshen iska da jiki ke buƙata domin rayuwa.

Olubunmi Tunji-Ojo
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo. Hoto: Olubunmi Tunji-Ojo
Source: Twitter

Maganar Ministan harkokin cikin gida

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya karɓi rahoton, ya yi alkawarin aiwatar da shawarwarin kwamitin domin tabbatar da adalci ga duk waɗanda lamarin ya shafa.

Ma'aikatar harkokin gida ta wallafa a X cewa ya umarci kwamandan hukumar NSCDC da ya dakatar da duk jami’an da suka yi aikin share wurin da aka tsare mutanen, bisa zargin cewa an yi hakan ne da nufin batar da sawu.

Kara karanta wannan

"Ba mu iya barci da idanu 2," Ɗan majalisa ya kai ƙorafin halin da suke ciki a mazaɓarsa

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin binciken ne a ranar 19 ga Satumba, bayan Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin gaskiya da riƙon amana kan mutuwar mutanen.

An yi hadarin mota a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane biyar, ciki har da ɗaliban makaranta maza huɗu da wata mata, sun mutu a wani mummunan haɗarin mota da ya shafi ayarin motocin Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin a unguwar Gidan Mangoro da ke kan hanyar Minna zuwa Bida, bayan wata motar Hilux da ke cikin ayarin gwamnan ta yi karo da wata mota kirar Peugeot 206.

Wani mazaunin yankin, Abdullahi Musa, ya shaida cewa haɗarin ya faru da misalin ƙarfe 11:35 na safe, lokacin da gwamnan da tawagarsa ke dawowa daga Bida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng