Matasa Sun Shiga Babbar Matsala da Suka Jefi Magoya bayan APC a Tawagar Gwamna

Matasa Sun Shiga Babbar Matsala da Suka Jefi Magoya bayan APC a Tawagar Gwamna

  • ’Yan sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da kai hari kan ayarin magoya bayan APC a hanyar Yashi zuwa Funtua da ke jihar Katsina
  • Harin ya yi sanadin lalata motoci da dama tare da jikkata wata mata da ke cikin motar haya
  • Kwamishinan ’yan sanda ya yi gargaɗin cewa ba za a lamunci daba ta siyasa da tashin hankali ba gabanin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - ’Yan sandan jihar Katsina sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da hannu a harkar daba ta siyasa.

An kama wadanda ake zargin ne bayan wani hari da aka kai wa ayarin magoya bayan APC da aka ruwaito suna cikin tawagar Gwamna Dikko Radda a kan hanyar Yashe zuwa Funtua, a ƙaramar hukumar Malumfashi.

Kara karanta wannan

Matasa sun kira sarki a waya, sun yi barazanar yin garkuwa da shi a Kano

Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sanda a bakin aiki a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Leadership ta rahoto cewa harin, wanda ya faru ranar Laraba yayin da ayarin ke kan hanyarsa ta zuwa Funtua domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe Gwamna Radda, ya yi sanadin lalata motoci da dama tare da jikkata wata mata.

Yan sanda sun kama mutane 14

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da kamen, inda ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11:00 na safe, ranar 28 ga Oktoba, 2026.

A cewarsa, rundunar ta tura jami’an tsaro zuwa muhimman hanyoyi, ciki har da hanyar Yashe zuwa Funtua, domin tabbatar da tsaron magoya bayan ’yan siyasa da sauran masu amfani da hanyoyin.

Ya bayyana cewa wasu da ake zargin ’yan daba ne, ɗauke da wuƙaƙe da duwatsu, sun taru a gefen hanyar tare da fara kai wa ayarin hari, da kuma motocin haya da ke wucewa.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun farfasa gilasan gaban motoci da dama, yayin da wata fasinja da ke cikin motar haya ta samu raunuka.

Aliyu ya ce jami’an ’yan sanda da aka girke a kan hanyar sun mayar da martani cikin gaggawa, sun maido da zaman lafiya tare da kama mutum 14 da ake zargi da hannu a harin.

Kwamishinan yan sanda ya yi Allah wadai

Kakakin rundunar ya bayyana cewa an gano wasu waɗanda ake zargi da hannu a harin da suka tsere daga wurin, inda ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke su.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya yi Allah wadai da harin.

APC Katsina.
Tawagar gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda lokacin da ta shiga garin Funtua Hoto: Ibrahim Kaula Mohammed
Source: Facebook

Ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan aikata abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci daba ta siyasa, tsoratarwa ko tashin hankali ba kafin lokacin yaƙin neman zaɓe, a lokacin gudanar da shi ko bayan kammalawarsa.

Yadda aka farmaki yan APC a Katsina

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Kun ji cewa magoya bayan APC sun ce wasu matasa sun kai musu hari a Katsina, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron yaƙin neman zaɓe a Funtua.

Waɗanda abin ya shafa sun shaida cewa suna cikin ayarin motocin Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, lokacin da wasu gungun matasa suka tare su tare da kai musu hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262