An Farmaki Yan APC yayin da Gwamna Radda Ya Kaddamar da Kamfen a Katsina

An Farmaki Yan APC yayin da Gwamna Radda Ya Kaddamar da Kamfen a Katsina

  • Magoya bayan APC sun ce wasu matasa sun kai musu hari a Katsina, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron yaƙin neman zaɓe a Funtua
  • Maharan sun lalata wayoyi, tufafi da motoci, tare da jikkata mutane da dama, lamarin da ya sa jami’an ’yan sanda suka shiga tsakani
  • Duk da rikicin, Gwamna Dikko Umaru Radda ya ci gaba da gabatar da nasarorin gwamnatinsa da ayyukan raya ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Malumfashi, Jihar Katsina – An samu tashin hankali a garin Malumfashi na Jihar Katsina bayan hari kan wasu magoya bayan jam’iyyar APC.

Yan jam'iyyar sun ce wasu matasa sun kai musu hari yayin da suke tafiya Funtua domin halartar taron yaƙin neman zaɓen Tinubu–Dikko ranar Laraba.

An farmaki yan APC a Katsina
Taswirar jihar Katsina da aka farmaki yan APC. Hoto: Legit.
Source: Original

Waɗanda abin ya shafa sun shaida cewa suna cikin ayarin motocin Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, lokacin da wasu gungun matasa suka tare su tare da kai musu hari, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Ana son ba da diyyar N1.4bn ga iyalan masu hakar ma'adinan da aka kashe a Neja

Mutane da yawa sun jikkata a harin

Lamarin ya jikkata mutane da dama, yayin da aka lalata kayayyakin wasu daga cikin magoya bayan, ciki har da wayoyin hannu, tufafi da sauran kayayyakin amfaninsu.

A cewar waɗanda abin ya shafa, maharan sun yi amfani da makamai masu haɗari wajen kai musu hari ba tare da wani dalili ko tsokana ba, har sai da jami’an ’yan sanda suka isa wurin suka tarwatsa matasan.

Wani daga cikin waɗanda suka jikkata ya ce:

“Mun kasance muna kan hanyarmu ta zuwa taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe lokacin da muka haɗu da wasu matasa masu fushi, waɗanda suka far mana da duwatsu da kwalabe. Mutane da dama sun ji rauni, sannan aka lalata mana kayayyaki.”

Waɗanda abin ya shafa sun yi kira ga hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da bincike tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake auka wa Kaduna, sun kuma yin garkuwa da bayin Allah

An ga duwatsu a hanyar Malumfashi

Rahoton ya bayyana cewa an ga duwatsu a warwatse a kan hanya kusa da zagayen gari na Malumfashi, a gefen babban masallacin Juma’a.

Haka kuma, an ruwaito cewa an lalata gilashin motocin wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa, lamarin da ya ƙara nuna irin barnar da ta faru a yankin.

Sai dai, har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin da aka ruwaito ba.

Radda ya ci gaba da yakin neman zabe

Duk da tashin hankalin da aka samu, Gwamna Dikko Umaru Radda ya ci gaba da gabatar da rahoton nasarorin gwamnatinsa mai taken Building Your Future.

Gabatarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.

An bayyana cewa yaƙin neman zaɓen a faɗin jihar zai mayar da hankali kan kai manufofin gwamnati da ayyukan raya ƙasa kai tsaye ga al’umma a yankunan sanatan Funtua, Daura da Katsina.

Kara karanta wannan

Ana jimamin Masussuka, 'yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun yi ta'addanci

Sai dai, rahoton bai bayyana ko an kama wani daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a harin ba.

Yan daba sun farmaki motocin dan takarar NDC

A baya, an ji cewa ’yan sanda a Ebonyi sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu uku bayan wani hari da ake zargin an kai wa ayarin motocin ɗan takarar NDC.

Ɗan takarar NDC a mazabar Ezza South ya ce wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai musu hari tare da ƙona motarsa kirar Toyota Hilux.

Offia-Nwali ya yi kira ga matasa da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cimma muradunsu na kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.