Tsohon Ministan Buhari Ya Kalubalanci Atiku kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur
- Babatunde Fashola ya ce Atiku Abubakar bai bayyana yadda zai samar da ɗanyen mai da ake buƙata domin dawo da tallafin man fetur ba
- Tsohon gwamnan ya nuna cewa matsalolin tsaro, satar ɗanyen mai da lalata bututun mai na kawo cikas ga cimma adadin da Najeriya za ta iya haƙowa.l
- Atiku ya bayyana a watan Agustan 2026 cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola, ya kalubalanci Atiku Abubakar da ya yi bayani kan yadda zai samar da kuɗaɗen dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.
Fashola ya bayyana shirin tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda ba shi da tushe mai ƙarfi, yana mai cewa Atiku bai yi cikakken bayani kan matsalolin da ka iya kawo cikas ga aiwatar da shirin ba.

Source: Facebook
Tsohon ministan ayyuka da gidajen a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels tv.
Ya ce matsalolin da suka haɗa da rashin cimma adadin haƙar ɗanyen mai da Najeriya ke da izinin samarwa, da kuma matsalar tsaro a yankunan da ake haƙar mai, na daga cikin abubuwan da ya kamata a yi la’akari da su.
Fashola ya tambayi inda za a samo ɗanyen man
Fashola ya ce akwai buƙatar Atiku ya bayyana inda zai samo ɗanyen man da za a bai wa matatun mai na cikin gida domin samar da man fetur da kuma aiwatar da tsarin tallafin.
Ya ce duk da kasancewar Najeriya na da matatun mai, ƙasar na fuskantar ƙalubalen samar da isasshen ɗanyen mai saboda matsalolin tsaro, satar mai da lalata bututun mai.
A kalamansa:
“Idan matatun mai suna aiki, mene ne adadin ɗanyen man da aka ware wa ƙasarmu a halin yanzu? Shin muna amfani da wannan dama yadda ya kamata? A’a, saboda akwai matsalolin da suka gada, da suka haɗa da matsalar tsaro da kuma lalata bututun mai.
“To, daga ina wannan ɗanyen man na al’ajabi zai fito? Ya kamata mutane su yi wannan tambayar.”
Ya ce Atiku na da damar bayyana cikakken bayani domin jama’a su tantance ko shirin nasa zai yiwu.
“Idan zai iya yin bayani, babu matsala, mutane su yanke hukunci. Amma idan babu hujja, kamar yin siddabaru ne,” in ji Fashola.
Ya ce sukar manufofin Atiku yake yi
Fashola ya jaddada cewa sukar da yake yi ba ta shafi Atiku a matsayinsa na mutum ba ce, illa shirin dawo da tallafin man fetur da ya gabatar.
"Shirin ba shi da tushe a zahiri. Ina duba shirin ne, ba halin mutumin da ya gabatar da shi ba.” In ji shi.
Ya kuma yi tambaya kan sauyin matsayar Atiku, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya goyi bayan cire tallafin man fetur a lokacin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Fashola ya ce wannan sauyin matsaya na buƙatar ƙarin bayani, musamman kan dalilin da ya sa Atiku ke son dawo da tallafin da a baya ya goyi bayan cirewa.
Dawo da tallafin zai buƙaci sauya doka
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa dawo da tallafin man fetur zai buƙaci a bi hanyoyin doka, domin Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta yi gyare-gyare ga dokokin da ake amfani da su a yanzu.
Ya yi tambaya kan ko ’yan majalisar za su amince da irin wannan mataki, la’akari da tasirin da zai iya yi ga kuɗaɗen gwamnati.
Fashola ya kuma yi amfani da gogewarsa a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, inda ya ce biyan tallafin man fetur ya taɓa rage kuɗaɗen da ake rabawa gwamnatocin jihohi.

Source: Twitter
Yadda Atiku zai dawo da tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zai sake duba yarjejeniyoyin da ake da su kan samar da ɗanyen mai, ciki har da waɗanda aka kulla domin karɓar rance.
Ya ce matakin zai taimaka wajen samar da isasshen ɗanyen mai ga matatun man fetur na cikin gida, a wani sabon tsarin tallafin man fetur da ya tsara bisa yawan man da ake samarwa.
Asali: Legit.ng


