El Rufai Ya Aiko da Sako Mai Zafi bayan Cika Kwanaki 256 a Tsare, Ya Ambaci Trump da Macron

El Rufai Ya Aiko da Sako Mai Zafi bayan Cika Kwanaki 256 a Tsare, Ya Ambaci Trump da Macron

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jawo hankalin shugabannin ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kan tsare shi
  • El-Rufai ya ce ya shafe kwanaki 256 a tsare, yana mai cewa yana da haƙƙin samun shari’a ta gaskiya da adalci
  • Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatarsa ta wanke shi ba tare da ya kare kansa ba, tare da ɗage shari’ar zuwa 25 ga Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya cika kwanaki 256 a tsare a hannun hukuma.

El-Rufai ya roƙi Shugaban Amurka, Donald Trump, da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, da sauran shugabannin ƙasashen duniya su jawo hankali kan ci gaba da tsare shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi Umrah a Saudiyya, ya bayyana addu'o'in da ya yi wa Najeriya

El-Rufai ya cika kwanaki 256 a tsare
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoban 2026, El-Rufai ya ce ya shafe kwanaki 256 a tsare, yana mai jaddada cewa ya cancanci a yi masa shari’a cikin adalci.

Ya bayyana cewa samun damar zuwa kotu da sauraron shari’a cikin adalci haƙƙoƙin ɗan Adam ne na asali, ba wasu gata ko alfarma da ake bai wa mutum ba.

El-Rufai ya ambaci Trump, Macron

A saƙon nasa mai taken #FairTrial, wato shari’a cikin adalci, tsohon gwamnan ya yi wa Trump da Macron alama kai tsaye, tare da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da Majalisar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ya kuma ambaci ƙungiyoyin Amnesty International, Tarayyar Turai (EU), da Tarayyar Afirka (AU), da wasu manyan kafafen yaɗa labaran duniya.

Cikin waɗanda ya yi wa alama har da fadar White House, gwamnatin Birtaniya, majalisar dokokin ƙasar da kafafen yaɗa labarai irin su CNN, BBC, Al Jazeera, The New York Times da The Economist.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

El-Rufai ya ce: “Shari’a cikin adalci ba wani aikin jinƙai ba ne. Ba gata ba ce. Haƙƙin ɗan Adam ne na asali.”

Matakin nasa na neman jawo hankalin ƙasashen duniya kan halin da yake ciki na fuskantar shari’a.

Kotun ta ki amincewa da buƙatar El-Rufai

Wannan roƙo na El-Rufai ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatarsa ta neman a wanke shi ba tare da ya gabatar da kariya ba.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce ta shigar da ƙarar laifin da ake tuhumarsa da shi, wanda ya shafi zargin satar sauraron tattaunawar wayar tarho ta mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ba bisa ƙa’ida ba.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik, a hukuncin da ta yanke ranar Litinin, 26 ga Oktoba, ta ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun hujjoji da suka wajabta wa El-Rufai ya gabatar da kariyarsa idan yana so.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

Lamarin ya samo asali ne daga wata hira da tsohon gwamnan ya yi da gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun 2026, inda ya yi magana kan zargin satar sauraron tattaunawar wayar Ribadu.

DSS ta shigar da ƙara a kansa bayan wannan hira, amma El-Rufai ya musanta zarge-zargen. Hukumar ta gabatar da shaidu biyu kafin ta kammala gabatar da nata shaidu a gaban kotu.

An dage shari’ar zuwa 25 ga Nuwamba

Bayan kammala gabatar da shaidun masu ƙara, El-Rufai ya buƙaci kotu ta wanke shi, yana mai cewa lauyoyinsa sun nuna cewa DSS ba ta kafa hujjar farko da za ta sa a ci gaba da shari’ar ba.

Sai dai kotun ta ƙi amincewa da buƙatar, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba domin fara sauraron kariyar wanda ake tuhuma.

El-Rufai na fuskantar wasu kararrakin

Baya ga ƙarar da DSS ta shigar, tsohon gwamnan na fuskantar wasu kararraki da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukan da Suka Shafi Hakan (ICPC) ta shigar a kansa.

Kara karanta wannan

Tafiyar Tinubu zuwa Makkah ta jawo masa abin da bai yi zato ba

Kararrakin sun shafi zargin cin hanci da rashawa da almundahana a harkokin kuɗi, dangane da wasu mu’amaloli da matakan da aka ɗauka a lokacin mulkinsa na shekaru takwas a jihar Kaduna, daga 2015 zuwa 2023.

El-Rufai na ci gaba da zama a tsare
Nasir El-Rufai ya kwashe kwanaki 256 a tsare Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Kotu za ta yanke hukunci a shari'ar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar yanke hukunci a karar da Nasir El-Rufai ya shigar kan hukumar ICPC.

Kotun ta sanya ranar 2 ga Disamba domin yanke hukunci kan karar N1bn da tsohon gwamnan na Kaduna, ya shigar kan Hukumar ICPC da wasu wadanda ake kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng