Shugaba Tinubu Ya Yi Umrah a Saudiyya, Ya Bayyana Addu'o'in da Ya Yi Wa Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Umrah a Saudiyya, Ya Bayyana Addu'o'in da Ya Yi Wa Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da aikin Umrah da safiyar Juma’a a Masallacin Harami da ke Makkah, Saudiyya
  • Tinubu ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya
  • Shugaban ƙasar ya roƙi Allah Ya ba shugabannin Najeriya hikima, tare da sa ƙasar ta samu ci gaban tattalin arziki da zamantakewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Makkah, Saudiyya - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gudanar da aikin Umrah da sanyin safiyar Juma’a a birnin Makkah mai alfarma da ke ƙasar Saudiyya.

Shugaban ƙasar ya yi addu’ar godiya ga Allah Madaukakin Sarki tare da roƙonSa Ya ci gaba da shiryar da Najeriya, Ya kuma kare ƙasar da al’ummarta.

Tinubu ya yi Umrah
Shugaba Bola Tinubu a wajen yin Umrah a Saudiyya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 30 ga Oktoban 2026 a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon APC ya yi wa Atiku tatas, ya bukaci ya yi ritaya daga siyasa

Tinubu ya zagaya Ka'aba a masallacin Harami

A yayin gudanar da ibadar, Tinubu ya zagaya ɗakin Ka'aba mai alfarma da ke cikin Masallacin Harami na Makkah, yana mai nuna biyayya, ibada da godiya ga Allah bisa ni’imomin da Ya yi wa Najeriya da al'ummarta.

Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida bayan kammala ibadar, shugaban ƙasar ya bayyana muhimmancin aikin Umrah da ya gudanar.

“Na yi imanin cewa wannan Umrah tana da matuƙar muhimmanci wajen nuna ƙaunar da muke yi wa al’ummarmu, jajircewarmu ga aikin da aka ɗora mana da kuma ƙasarmu Najeriya.
“Haka kuma, tana nuna biyayyarmu ga nufin Allah, cewa kalmarSa ce za ta yi rinjaye, kuma babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Shi kaɗai ne ke ƙaddara abin da mutum zai zama da kuma makomarsa a rayuwa.” In ji shi.

Ya yi addu’ar samun zaman lafiya da hadin kai

Shugaba Tinubu ya roƙi Allah Ya azurta Najeriya da zaman lafiya mai ɗorewa, haɗin kan ƙasa, fahimtar juna da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Atiku v Amaechi: Wike ya lissafo matsaloli da ke tattare da tikitin ADC

Ya kuma roƙi Allah Ya shiryar da shugabannin ƙasar, Ya ba su hikimar tafiyar da al’amuran jama’a, tare da ƙarfafa zumunci da ’yan’uwantaka tsakanin ’yan Najeriya.

Haka kuma, ya yi addu’ar Allah Ya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar.

Tinubu ya ce yana godiya ga Allah bisa damar da Ya ba shi na gudanar da Umrah, inda ya bayyana cewa sun yi addu’a domin kowa a Najeriya ya rayu cikin zaman lafiya, farin ciki da imani da Allah.

Tinubu ya gudanar da Umrah a Saudiyya
Shugaba Tinubu na gaisawa da Abdulsamad Rabiu a Makkah Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya yi fatan Najeriya ta samu ci gaba

Shugaban ƙasar ya bayyana fatan cewa Najeriya za ta ci gaba da samun ci gaba a fannin tattalin arziki, bunƙasar zamantakewa da samar da makoma mai aminci ga dukkan 'yan ƙasar.

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na gina ƙasa mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata, inda kowane ɗan Najeriya zai samu damar rayuwa cikin tsaro da mutunci.

Tinubu ya ce burin gwamnatinsa shi ne ganin cewa babu bambancin addini ko asali da zai hana kowane ɗan ƙasa rayuwa cikin mutunci, aminci da fahimtar juna.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kawar da shakkun 'yan Najeriya, ya fadi dalilinsa na runtumo basussuka

APM ta kalubalanci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APM ta ƙalubalanci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana ainihin inda zai je.

APM ta bayyana cewa ya kamata ya zauna a Najeriya domin yi wa ƙasar addu’a tare da magance matsin rayuwar da jama’a ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng