Tsugunne ba Ta Kare ba; El Rufai Ya Samu Koma Baya a Kotu
- Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da bukatar El-Rufai ta cewa babu isassun hujjojin da za su sa a bukaci ya kare kansa
- Gwamnatin Tarayya ta rufe gabatar da shari’arta bayan ta gabatar da shaidu biyu, kafin tsohon gwamnan ya shigar da bukatar neman a sallami karar
- Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, domin El-Rufai ya fara gabatar da hujjojin kariyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na cewa babu isassun hujjojin da za su sa a bukaci ya kare kansa.
Kotun ta yi watsi da bukatar ne a shari’ar da ake yi masa kan zargin kutse ba bisa ka’ida ba a bayanan kiran waya.

Source: Twitter
Kotu ta ki amincewa da bukatar El-Rufai
Jaridar Daily Trust ta ce a hukuncin da ta yanke ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026, kotun ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji da za su sa a bukaci wanda ake tuhuma ya bayyana matsayinsa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Saboda haka, mai shari’a Joyce Abdulmalik ta umarci tsohon gwamnan da ya fara gabatar da kariyarsa, inda ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba.
El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume guda biyar da aka yi wa kwaskwarima, wadanda Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta shigar kan zargin kutse a bayanan kiran waya da ke da alaka da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Yadda zargin ya samo asali
A watan Fabrairun 2026, yayin wata hira da shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, El-Rufai ya ce wani mutum ne ya kutsa cikin wayar Ribadu, lamarin da ya ba shi damar jin wani umarni da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya bai wa jami’an tsaro na su kama shi.
Bayan Gwamnatin Tarayya ta gabatar da shaidu biyu a gaban kotu, ta rufe bangaren gabatar da hujjojinta. Daga nan ne El-Rufai ya shigar da bukatar neman a sallame shi ba tare da ya gabatar da kariya ba.
Lauyoyin bangarorin sun yi muhawara
Yayin sauraron bukatar a ranar Litinin, lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, wanda babban lauya ne mai mukamin SAN, ya roki kotun da ta sallami tsohon gwamnan tare da wanke shi daga tuhume-tuhume biyar da ake yi masa, The Punch ta kawo labarin.
Paul Erokoro ya bayar da hujjar cewa masu gabatar da kara ba su kafa hujjojin farko da za su isa a tilasta wa El-Rufai ya kare kansa ba.
Sai dai lauyan masu gabatar da kara, Oluwole Aladedoye, ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar, yana mai cewa shaidun baki da takardun da aka gabatar sun isa a bukaci wanda ake tuhuma ya amsa zarge-zargen.
Bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, Mai shari’a Abdulmalik ta yanke hukunci a kan bukatar, inda ta amince da matsayar masu gabatar da kara.

Source: Twitter
El-Rufai ya sumbaci matarsa a kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani bidiyo ya nuna tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana sumbatar matarsa bayan isarsu Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
Lamarin ya dauki hankulan jama’a a daidai lokacin da ake ci gaba da shari’ar da gwamnatin tarayya ta shigar a kansa.
Asali: Legit.ng

