Canje canje 6 da aka yi wa aikin kwamitin zaben Bola Tinubu yayin da ake cikin kamfe
- Bayan an sanar da nada kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, jam’iyyar APC ta yi wasu garambawul a majalisar
- An kara adadin mutane kuma an samu karin wasu kwamitocin da za su taya Bola Tinubu/Kashim Shettima yin kamfe
- Ta kai an sauya jihohin da shugaban kasa zai ziyarta da kan shi, adadin wuraren da zai je sun kara yawa daga 12 zuwa 20
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC a zaben 2027 ya ci karo da wasu sauye-sauye daga Agustan 2026 zuwa yanzu.
Daga wancan lokaci da aka sanar da ‘yan kwamitin kamfen zuwa yau, an ga karin kwamitoci da saka sunan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyun hamayya.
Wanda ya ga rubutun nan zai ga irin sauye-sauyen da kwamitin yakin zaben Bola Tinubu ya samu.
Da farko an fitar da cikakken sunayen ‘yan kwamitin a Agustan 2026 amma sai aka koka da cewa akwai wasu fitattun ‘yan APC da aka manta da su.
APC da kan ta, ta nuna akwai yiwuwar a samu kare-kare domin a tafi da kowa wajen harkar kamfe.
1. Kare-karen manyan APC da ‘yan adawa
A tsakiyar Oktoba kwamitin yakin neman zaben ya cusa sunayen irinsu Ministan Abuja da wasu gwamnonin jam’iyyun adawa kuma aka ba su mukamai.
- Nyesom Wike
- Ademola Adeleke
- Chukwuma Soludo
- Sheriff Oborevwori
- Abdullahi Ganduje
- Festus Keyamo
- Joseph Yobo
- Babatunde Fashola
- Benjamin Kalu
- David Umahi
- Abdulmumin Jibrin.
2. Karin sababbin sassa da wasu sauye-sauye
Daga nan kuma The Cabe ta rahoto cewa an kirkiri wasu sababbin sassa kuma aka nada masu shugabanni, mataimakansu da kuma sakatarori.
A ranar 20 ga watan Oktoba 2026 muka samu labarin wadannan canje-canje da aka yi a APC-PCC.
- Farouk Aliyu – Darektan shirya mimbarori da duron siyasa
- Adejare Bello – Dayan Darektan shirya mimbarori da duron siyasa
- Ayodele Olawande – Darektan sashen tattaro matasa.
- Dayo Israel – Mataimakin Darektan sashen tattaro matasa.
- Mary Aille Idele – Darektan sashen tattaro mata.
- Betta Edu – Mataimakiyar Darektar sashen tattaro mata.
- Imaan Suleman – Sakatariyar sashen tattaro mata.

Kara karanta wannan
Wike ya maida wa Amaechi martani da ya ji ana lissafin wuraren da Atiku zai ci zabe
3. Karin sababbin sassa
Bayan nan kuma TVC ta rahoto wasu kare-kare da aka samu dangane da ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na jam’iyyar APC.
Ranar 28 ga Oktoba, Sakataren APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru ya ce sun fito da bangarorin:
- Kula da lura da zabe
- Dabarun sadarwa na zamani
- Tsaro da sa ido
- Nishadi da wasanni
- Kungiyoyi masu zaman kan su
- Kiwon lafiya da ilmi
- Tattaro matasa
- Kungiyoyin addinai da na kwadago
- Jin kai da tattaro ‘yan majalisa
4. Garambawul a wajen sha’anin sadarwa
A ranar 11 ga Nuwamba 2026, sanarwa ta fito daga Femi Gbajabiamilla cewa mutane uku kadai aka amince su yi magana a matsayin kakakin kwamitin kamfe.
Wadannan mutane su ne:
· Abdulaziz Yari
· Dele Alake
· Mohammed Idris
5. Karin jihohin da Bola Tinubu zai ziyarta
Mako daya bayan nan kuma sai The Cable ta fitar da labari cewa an kara adadin wuraren da shugaban kasa zai ziyarta daga 12 zuwa 20.
A yanzu Bola Tinubu zai taka da kafafunsa ya yi kamfe a jihohi 19 da kuma birnin tarayya Abuja. Wuraren da aka kara bayan an cire Bauchi su ne:
- Katsina
- Taraba
- Zamfara
- Imo
- Kwara
- Akwa Ibom
- Jigawa
- Kebbi
- Abuja
Dama can zuwa yanzu shugaba Tinubu ya ziyarci wasu jihohin da aka kara – Jigawa, Kebbi da Akwa Ibom.
Asali: Legit.ng

