Rana ba Ta Karya: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci a Shari'ar El Rufai da ICPC

Rana ba Ta Karya: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci a Shari'ar El Rufai da ICPC

  • Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta sanya ranar 2 ga Disamba domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar
  • El-Rufai na zargin jami’an ICPC da ’yan sanda da keta hakkokinsa bayan binciken gidansa da ke Abuja a watan Fabrairu
  • Lauyoyin ICPC, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Ministan Shari’a sun bukaci kotun ta yi watsi da karar gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar yanke hukunci a karar da Nasir El-Rufai ya shigar kan hukumar ICPC.

Kotun ta sanya ranar 2 ga Disamba domin yanke hukunci kan karar N1bn da tsohon gwamnan na Kaduna, ya shigar kan Hukumar ICPC da wasu wadanda ake kara.

Kotu za ta yanke hukunci a shari'ar El-Rufai da ICPC
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

Mai shari’ar ta sanya ranar ne bayan lauyoyin bangarorin sun gabatar tare da amincewa da takardun shari’arsu a gaban kotun, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Isa Ashiru ya fito da gaskiyar zance bisa zargin ya fallasa El Rufai kan rashin tsaro a Kaduna

Abin da ya faru a zaman kotun

A lokacin da aka kira karar, lauyan El-Rufai bai halarci kotun ba. Saboda haka, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar da umarnin daukar duk takardun da tsohon gwamnan ya shigar a matsayin wadanda ya riga ya amince da su.

Lauyan ICPC, Abdul Mohammed, SAN, ya bayyana tare da amincewa da takardun, sannan ya bukaci kotun ta yi watsi da karar gaba daya.

Haka kuma, ACP Ezekiel Rimamsomte, wanda ya wakilci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, da Maimuna Lami-Shiru, wadda ta wakilci Antoni Janar na Tarayya, sun gabatar da takardunsu. Dukkansu sun roki kotun ta yi watsi da karar El-Rufai.

A yayin zaman, lauyan tsohon gwamnan, Ubong Akpan, ya shigo kotun, inda ya nemi afuwa saboda jinkirin da ya yi.

Lokacin da ya nemi izinin gabatar da takardun shari’arsa, alkalin ta sanar da shi cewa tuni ta bayar da umarnin daukar takardun a matsayin wadanda aka amince da su.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan wani matashi da ya yi barazanar sakin hotunan tsiraicin Gwamna Abba

Daga nan ne Mai shari’a Abdulmalik ta dage karar zuwa ranar 2 ga Disamba domin yanke hukunci.

Dalilin da El-Rufai ya shigar da karar

El-Rufai ya shigar da karar ne kan ICPC, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da Antoni Janar na Tarayya, inda yake neman a biya shi N1bn a matsayin diyya.

Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa jami’an ICPC da na ’yan sanda sun take masa hakkokinsa bayan gudanar da bincike a gidansa da ke Abuja a watan Fabrairun 2026.

Ya bukaci kotun ta ayyana cewa kutsawa da binciken gidansa da ke House 12, Mambilla Street, Aso Drive, Abuja, ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

A cewar El-Rufai, binciken ya faru ne ranar 19 ga Fabrairu da misalin karfe 2:00 na rana, kuma jami’an ICPC da na ’yan sanda ne suka gudanar da shi.

Ya kuma bukaci kotun ta bayyana cewa matakin ya keta hakkinsa na mutunci, ’yancin kai, samun adalci a shari’a da kuma sirrin rayuwa, kamar yadda sashe na 34, 35, 36 da 37 na kundin tsarin mulkin Najeriya suka tanada.

Kara karanta wannan

Sojoji sun toshe kofofin tsira ga 'yan ISWAP, an kashe babban kwamanda da wasu mayaka

Kotu za ta yanke hukunci kan karar El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Kotu ta ba El-Rufai umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Joyce Abdulmalik, ta ba Nasir El-Rufai, umarni.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta umarci tsohon gwamnan jihar Kaduna da ya gabatar da kariyarsa idan yana so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng