Tafiyar Tinubu zuwa Makkah Ta Jawo Masa Abin da Bai Yi Zato ba
- Jam’iyyar APM ta ƙalubalanci Shugaba Tinubu da ya bayyana ainihin inda zai je, tana mai cewa bai kamata ya yi tafiya zuwa Umrah ba
- Kakakin yaɗa labaran jam’iyyar, Abubakar Yusuf, ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙara tsananta matsin rayuwa, tare da kira ga shugaban ya zauna ya magance matsalolin jama’a
- APM ta yi ikirarin cewa Tinubu na iya fuskantar matsala wajen samun kashi 25 na ƙuri’u a jihohi 12 a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APM ta ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana ainihin inda zai je, tana mai cewa ya kamata ya zauna a Najeriya domin yi wa ƙasar addu’a tare da magance matsin rayuwar da jama’a ke ciki.
Jam’iyyar APM ta ce ya kamata shugaban ƙasar ya mayar da hankali kan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya maimakon tafiya ƙasar waje.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin APM na kasa, Abubakar Yusuf, ya fitar a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban, 2026. APM ta kuma nuna shakku kan tafiyar da aka bayyana cewa zai yi domin gudanar da ƙaramin aikin Umrah.
APM ta yi shakku kan dalilin tafiyar Tinubu
A cikin sanarwar, Abubakar Yusuf ya tambayi dalilin tafiyar shugaban ƙasar, yana mai cewa bai kamata a yi amfani da ibadar Umrah wajen kawar da hankalin jama’a daga matsalolin da suke fuskanta ba.
“Umrah ibada ce da ta ƙunshi addu’a da roƙon Allah, amma ba dama ba ce ta yin abubuwan da ba a saba yi ba ko kuma ta zama abin ɓoye wasu ayyuka.” In ji shi.
Kakakin jam’iyyar ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙara tsananta wahalar rayuwa a ƙasar, yana mai cewa ya kamata shugaban ya zauna domin magance matsalolin talakawa.
Ya ƙara da cewa:
"Ba za ka yi addu’a kan matsalolin da kai da kanka ka jefa talakawa a ciki ba, alhali kana iya zama a nan ka magance matsalolin da suka yi wa jama’a yawa, waɗanda aka ƙirƙira ta hanyar manufofin da ake bi.”
APM ta yi hasashen zaɓen 2027
Yayin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara matsowa, Abubakar Yusuf ya yi ikirarin cewa Tinubu na iya fuskantar ƙalubale wajen samun kashi 25 na ƙuri’un da ake buƙata a jihohi 12 da ya ambata.
Ya ƙalubalanci shugaban ƙasar da ya kula da matsayinsa a siyasa da kuma damar da yake da ita ta samun nasara a zaɓen mai zuwa.
Kakakin APM ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Seyi Makinde, zai kayar da Tinubu a 2027.
Ya bayyana Makinde a matsayin ɗan siyasa mai ƙwazo da kuzari, wanda a cewarsa zai iya ƙalubalantar ƙarfin siyasar Tinubu a yankin Kudu maso Yamma da sauran sassan Kudancin Najeriya.

Source: Twitter
Abin da zai kai Tinubu Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai Shugaba Bola Tinubu shawara kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya musanta zargincewa shugaban kasa zai je kasar Saudiyya ne domin a duba lafiyarsa.
Dada Olusegun bayyana cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu zai tafi Saudiyya ne domin gudanar da Umrah, ba wai neman magani ba.
Asali: Legit.ng


