Kotu Ta ba El Rufai Sabon Umarni bayan Kin Amincewa da Bukatarsa

Kotu Ta ba El Rufai Sabon Umarni bayan Kin Amincewa da Bukatarsa

  • Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ba tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, umarni a shari'ar da ake yi
  • Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, domin El-Rufai ya samu damar kare kansa kan zargin kutse a bayanan kiran wayar Nuhu Ribadu
  • Hakan na zuwa ne mako guda bayan wata kotun FCT ta yi watsi da karar El-Rufai ta neman diyyar naira miliyan 120 kan wasu hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya gabatar da kariyarsa idan yana so.

Kotun ta bayar da umarnin ne a ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin kutse ba bisa ka’ida ba a bayanan kiran wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Ana zargin Ebola ta ci gaba da yaduwa a Najeriya, NCDC ta gano mutane 53 da suka yi mu'amala

Kotu ta ba El-Rufai umarni
Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Wane umarni kotu ta ba El-Rufai?

Tashar Channels tv ta ce alkalin ta bayar da wannan umarni ne yayin yanke hukunci kan bukatar El-Rufai, inda yake neman kotu ta yi watsi da shari’ar saboda a cewarsa, masu gabatar da kara ba su gabatar da isassun hujjoji da za su sa a bukaci ya kare kansa ba.

Sai dai mai shari’a Abdulmalik ta yi watsi da bukatar, tana mai cewa masu gabatar da kara sun gabatar da hujjojin da suka isa a bukaci wanda ake kara ya bayyana matsayinsa idan yana son yin hakan.

Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, domin El-Rufai ya gabatar da kariyarsa, Arise News ta kawo labarin.

Wannan mataki yana nufin cewa tsohon gwamnan ya samu damar mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi masa yayin da shari’ar ke ci gaba. Sai dai umarnin kotun ba yana nufin an tabbatar da laifinsa ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi amfani da tafiya kamfen Tinubu, sun tafka mummunan ta'adi a Zamfara

Wata kotu ta yi watsi da karar El-Rufai

A wani lamari mai alaka da shari’o’in da El-Rufai ke fuskanta, wata Kotun Babbar Shari’a ta Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin jagorancin Mai shari’a Sylvanus Oriji, ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan ya shigar yana neman diyyar Naira miliyan 120 daga hukumomin gwamnati.

Hukumomin da karar ta shafa sun hada da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukan da Suka Shafi Hakan (ICPC), da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya.

Kotun ta bayyana cewa matakan da hukumomin suka dauka, ciki har da gayyatar El-Rufai, yunkurin kama shi a filin jirgin sama da kwace fasfo dinsa, ba su saba wa hakkokinsa na asali ba.

Haka kuma, kotun ta umarci kowanne daga cikin wadanda aka shigar da karar da su samu diyyar kashe-kashen shari’a na naira 200,000.

Kara karanta wannan

Tinubu na Kaduna, El Rufai ya jefa masa tambayoyi 12, ya tuna masa hadisin Manzo

El-Rufai na fuskantar wasu shari’o’i

Baya ga shari’ar da ta shafi zargin kutse a bayanan kiran wayar Ribadu, El-Rufai na fuskantar wasu shari’o’i da ke ci gaba da gudana.

Daga cikinsu akwai shari’o’in da suka shafi zargin cin hanci da rashawa da safarar kudaden haram, wadanda ke da alaka da binciken ICPC a jihar Kaduna.

El Rufai bai samu yadda yake so ba a kotu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

An dage shari'ar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Kaduna ta ɗage shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Kotun ta dage shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan ne kan zargin karkatar da kuɗin gwamnati zuwa ranakun 30 ga Nuwamba da 1 ga Disamba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng