Yadda Yan Bindiga Suka Kafa Gwamnatinsu, Suke Karbar Haraji Kala 3 a Jihohin Arewa 2

Yadda Yan Bindiga Suka Kafa Gwamnatinsu, Suke Karbar Haraji Kala 3 a Jihohin Arewa 2

  • ’Yan bindiga sun ƙirƙiri tsarin karɓar haraji iri uku a jihohin Zamfara da Sokoto, lamarin da ke tilasta wa manoma barin gonakinsu
  • Ana karɓar kuɗin da suka kai Naira miliyan 4 zuwa miliyan 6 daga kowace al’umma a Sabon Birni kafin a bar manoma su shiga gonakinsu
  • Ƙungiyar manoman shinkafa ta Zamfara ta ce jihar na asarar Naira biliyan 43 duk shekara, yayin da ake hasashen noman shinkafa zai ragu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Daga abin da ya fara a matsayin hare-haren yan bindiga na lokaci-lokaci kan manoma a jihohin Zamfara da Sokoto ya rikide zuwa mamaye yankuna.

Rahotanni sun nuna yadda ’yan bindiga suka kafa tsarin karɓar haraji na kansu, wanda ke durƙusar da noma tare da ƙara tsadar abinci a Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Magana ta fara fitowa, an ji dalilin da ya sa Tinubu ke son karbo bashin kusan Naira tiriliyan 30

Oluyede.
Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede Hoto: DHQNigeria
Source: Twitter

Wani bincike da jaridar Leadership ta gudanar a jihohin biyu ya gano cewa ’yan bindiga sun kafa tsarin karɓar kuɗaɗe iri uku daga manoma.

Tsarin ya haɗa da kuɗin da ake karɓa kafin fara noma, harajin amfanin gona lokacin girbi da kuma kuɗin kariya.

Wannan al’amari ya tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu saboda tsoron hare-hare, sacewa da kuma kashe-kashe.

Harajin Naira miliyan 4 zuwa 6

A watan Yuni na 2026, an ce ’yan bindiga sun kakaba sabon haraji ga aƙalla kauyuka 26 a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Kauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Zululu, Garin Faji, Cinnah Barka, Dan Gari, Garin Idi, Garin Maigayya, Gardi, Katsira, Garin Baushe, Sulmawa, Zakin Ganga da Kaifin Aska, da sauransu.

Wani mazaunin Garin Faji, Zayyanu Biri, ya shaida wa LEADERSHIP cewa ’yan bindigar sun buƙaci kowane gari ya biya tsakanin Naira miliyan 4 da miliyan 6 kafin a ba manoma damar shiga gonakinsu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Ya ce ana karɓar gudummawar tsakanin N1,500 da N2,000 daga kowane gida, yayin da manyan manoma ke biyan har N5,000.

Hakazalika, wani dagacin ƙauyen Tsamaye, Isiyaka Dangaladima, ya ce manoma a ƙauyukan da ke ƙarƙashin ikonsa sun shafe kusan shekaru huɗu suna biyan kuɗaɗe ga wani shugaban dvar ’yan bindiga da aka bayyana da sunan Yar Daribiyar.

Ya ce:

“Yayin da manoma ke aiki a gonakinsu, ’yan bindiga kan kai hare-hare lokaci zuwa lokaci domin yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, sannan a wasu lokutan su kashe mutane cikin zalunci."

Naira miliyan 50 bayan harin sojoji

A yankin Dansadau da ke ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ana zargin ’yan bindiga ƙarƙashin jagorancin wani Dankarami Gwaska da kakaba harajin Naira miliyan 50 ga al’ummar Bindin da maƙwabtanta.

An ce sun ɗauki matakin ne bayan wani hari da aka kai sansanin sojoji a yankin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an karɓi kuɗaɗen da suka kai kusan Naira miliyan 360 cikin makonni biyu bayan harin, wanda ya jawo ƙonewar gidaje da shaguna.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

A ƙaramar hukumar Tsafe kuwa, tsarin ya ɗan bambanta. A nan, garuruwa na biyan harajin girbi tsakanin Naira miliyan 5 da miliyan 20 kafin a ba su damar girbe amfanin gonakinsu.

Sai dai abin damuwa shi ne, ko bayan biyan kuɗaɗen, ’yan bindigar kan saki shanunsu su shiga gonakin su lalata amfanin gonar.

Dauda Lawal.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da Gwamna Ahmed Aliyu na Sakkwato Hoto: Dauda Lawal, Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Asarar biliyoyin Naira da tsadar abinci

Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) a Zamfara ta bayyana cewa jihar na asarar kuɗaɗen shiga daga noma da suka kai kusan Naira biliyan 43 duk shekara.

Ƙungiyar ta kuma yi hasashen cewa noman shinkafa zai ragu da kashi 50 cikin 100 a wannan kakar noma.

Masana sun kuma danganta tsarin karɓar kuɗaɗen da ’yan bindiga suka kafa da hauhawar farashin abinci.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa masu jigilar kayan abinci yanzu suna biyan kuɗin da ya kama daga N5,000 zuwa N50,000 a kowace tafiya, wanda ake kira kuɗin kariyar sufuri.

An ce waɗannan ƙarin kuɗaɗe suna ƙara farashin kayan abinci a kasuwanni da kashi 20 zuwa 30 cikin 100, lamarin da ke ƙara wa al’umma nauyin tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Taimakon da gwamnatin Tinubu ta nema kan shirin yan sanda jihohi a Najeriya

Yan bindiga sun kashe dakarun JTF

Kun ji cewa yan bindiga sun kashe mambobin rundunar sa-kai ta JTF guda bakwai, tare da sace mazauna garin Kaura Namoda 38 a Jihar Zamfara.

Ana zargin cewa tafiyar jami’an tsaro zuwa Kaduna domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya taimaka wa ’yan bindigar kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262