'Yan Bindiga Sun Tare 'Yan Kasuwar da Ke Samun Rakiyar Sojoji a Zamfara, an Rasa Rayuka
- ShaAna fargabar aƙalla mutum 22 sun mutu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kan ’yan kasuwa a jihar Zamfara
- Lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi, lokacin da ’yan kasuwar ke tafiya daga Gurusu zuwa Gwashi domin halartar kasuwar mako-mako
- Har zuwa lokacin kammala rahoton, rundunar sojin Najeriya da rundunar ’yan sandan Zamfara ba su fitar da sanarwar hukuma kan harin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Ana fargabar aƙalla mutum 22 sun mutu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi wa ’yan kasuwa kwanton ɓauna a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun yi wa 'yan kasuwan kwanton bauna ne okacin da sojojin Najeriya ke raka su zuwa kasuwa.

Source: Original
Jaridar Leadership ta ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoban 2026 yayin da ’yan kasuwar ke tafiya daga Gurusu zuwa Gwashi, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum, domin halartar kasuwar mako-mako a Gwashi.

Kara karanta wannan
Mutane sun fusata bayan 'yan sanda sun hana 'yan 'Tinubu Must Go' yin taro a Kano
An ce jami’an tsaro na cikin waɗanda aka kashe
Wani mazaunin yankin, Malam Aminu Gwashi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane da dama a harin, ciki har da wasu jami’an tsaro yayin harin.
Ya ƙara da cewa wasu mutane da dama sun samu raunuka, kuma an garzaya da su Babban Asibitin Bukkuyum domin ba su kulawar likitoci.
Sai dai, ba a samu cikakken bayani kan adadin waɗanda suka mutu ko waɗanda suka jikkata ba daga hukumomin tsaro.
Hare-haren ’yan bindiga na ci gaba da shafar al’umma
Al’ummomin Gwashi da Bukkuyum sun sha fuskantar hare-haren ’yan bindiga a ’yan kwanakin nan, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da sauran ayyukan tattalin arziki a yankin.
Hare-haren sun kasance ƙalubale ga mazauna yankin, musamman wajen gudanar da harkokin yau da kullum da zirga-zirgar ’yan kasuwa.
Sojoji da ’yan sanda ba su fitar da sanarwa ba

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan ta'adda suka hallaka sojoji da dan kasar waje a Kebbi
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar sojin Najeriya bai yi nasara ba, domin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Aliyu Danja, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
Haka kuma, Jami’in Yaɗa Labarai na runduna ta 8, Manjo Osoba Olaniyi, bai amsa kiran da aka yi masa domin tabbatar da faruwar lamarin ba.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya da rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ba su fitar da sanarwa a hukumance kan harin ba.

Source: Facebook
Sojoji sun gano bama-bamai a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun Operation Fansan Yamma sun gano tare da lalata bama-bamai da 'yan ta'adda suka dasa a kan hanyar Magami-Hannutara-Dansadau, da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Dakarun sun dauki matakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan abubuwan fashewar da aka dasa domin haddasa babbar barna ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.
Asali: Legit.ng