Magana Ta Fara Fitowa, An Ji Dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Karbo Bashin kusan Naira Tiriliyan 30

Magana Ta Fara Fitowa, An Ji Dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Karbo Bashin kusan Naira Tiriliyan 30

  • Ministan kuɗi, Taiwo Oyedele ya yi karin haske kan dalilin da ya sa gwamnatin tarayya za ta sake karbi bashin Naira tiriliyan 30
  • Ya bayyana cewa kudin da karin nauyi ba ne ga Najeriya domin za a yi amfani da su ne wajen zuba jari a bangarorin tattalin arziki
  • Oyedele ya ce shirin ba yana nufin gwamnati ta karɓi bashin gaba ɗaya ba, domin matsakaicin lokacin kammala ayyukan shi ne shekara biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya kare buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta neman sake karbi bashi daga kasashen waje.

Bayanaij Oyedele na zuwa ne bayan Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Tarayya domin karɓar rancen kuɗaɗen ƙasashen waje da suka kai Dala biliyan 20.52 da kuma Yuro biliyan 1.045.

Kara karanta wannan

Bashin da ake bin Najeriya ya yi haramar kai Naira tiriliyan 200 a karkashin Tinubu

Oyedele.
Ministan harkokin kudi kuma mai kula da tattalin arzikin kasa, Taiwo Oyedele Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa Oyedele ya bayyana cewa za a zuba kuɗaɗen ne a muhimman sassa na tattalin arzikin ƙasar domin bunƙasa su da kuma samar da kadarori da za su amfani Najeriya.

Tinubu zai sake karbo bashi daga waje

A ranar Talata ne Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar Tinubu a zauren majalisar, inda shugaban ƙasar ya nemi amincewa da ƙarin shirin karɓar rancen ƙasashen waje.

Buƙatar ta jawo suka daga wasu mutane, musamman saboda gwamnatin tarayya ba ta bayyana takamaiman ayyukan da za a kashe kuɗaɗen a kansu ba.

Sai dai Oyedele ya bayyana muhimman fannoni da za su amfana da kuɗaɗen yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Tinubu ya jagoranta.

Fannonin da za a zuba kuɗaɗen

Ministan ya bayyana cewa shirin ya shafi zuba jari ne maimakon a kira shi aron kuɗi na yau da kullum, yana mai cewa manufar ita ce samar da kadarori da dukiya ga ƙasar.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi wa Tinubu zafafan tambayoyi kan ciwo bashin $20bn da £1bn

Ya ce idan aka haɗa kuɗaɗen Dala da na Yuro, adadin zai kai kusan dala biliyan 21.7, kimanin Naira tiriliyan 30 a kudin gida Najeriya

Oyedele ya jaddada cewa gabatar da shirin ba yana nufin gwamnati ta karɓi duk kuɗaɗen ba, ko kuma za ta karɓe su gaba ɗaya.

"Mun ga wasu na cewa gwamnati za ta karɓi wannan da wancan a matsayin bashi. Ina farin cikin sanar da ku cewa a zahiri, wannan bai cancanci a kira shi rance ba. Wannan zuba jari ne," innjinshi.

Ministan ya ce Najeriya na buƙatar yin tsare-tsare tun da wuri, maimakon gudanar da al’amura ba tare da kyakkyawan shiri ba, kamar yadda tashar Channels ta rahoto.

Oyedele.
Ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Taiwo Oyedele tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock Hoto: Taiwo Oyedele
Source: Facebook

Ya lissafa fannoni 10 da za su fi samun kaso daga rancen, waɗanda suka haɗa da sufuri, tsaro da yaƙi da laifuffuka, lafiya, noma, da kuma makamashi.

Sauran bangarorin su ne wutar lantarki, kayayyakin more rayuwa, harkokin kuɗi da ƙananan masana’antu da matsakaitan sana’o’i (MSMEs), tallafin jin ƙai, muhalli da ilimi.

Adadin bashin da ake bin Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirin karɓar bashi daga kasar waje.

Idan shugaban kasar ya samu yadda yake so, jimillar bashin Najeriya na iya haura Naira tiriliyan 200 kafin ƙarshen 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262