"Bai Cancanta ba," An Tono Abin da Zai Iya Zama Matsala ga Abokin Takarar Atiku a 2027
- Nyesom Wike ya bukaci ’yan Najeriya da kada su zaɓi tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, a kowane muƙami bisa zargin almundahanar kuɗaɗe
- Wike ya yi zargin cewa ba a san inda Dala miliyan 308 da aka samu daga sayar da tashar wutar lantarki ta Afam a 2014 suka shiga ba
- Ministan ya kuma tambayi inda aka kai Dala miliyan 49 na asibitin Justice Karibi-Whyte da kuma Naira biliyan 68 na aikin jirgin ƙasa na cikin gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya ce bai kamata a zaɓi tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi a matsayin mataimakin shugaban kasa ba.
Wike ya ce ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC. Rt. Hon. Chibuike Amaechi, bai cancanci rike kowane muƙami a ƙasar ba saboda zargin rashin kyakkyawan kula da kuɗaɗen gwamnati.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bikin buɗe taro da miƙa tutoci ga ’yan takarar da ƙungiyar Rainbow Coalition ta zaɓa a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Manyan jiga-jigan da suka je taron Wike
Manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Mao Ohuabunwa, da shugaban hukumar kula da harkokin mai ta NUPRIC, Sanata Magnus Abe.
Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban APC na ƙasa mai kula da shiyyar Kudu maso Kudu, takwaransa na PDP, Hon. Aaron Chukwuemeka, da tsohon sakataren gwamnatin jihar Rivers, Dakta Tammy Danagogo.
Sai dai shugaban APC na jihar, Cif Tony Okocha, bai halarci bikin buɗe taron ba, duk da cewa dubban magoya baya da mambobin jam’iyyun siyasa shida da suka haɗa da Rainbow Coalition sun halarta.
Dalilin da ya sa Amaechi bai cancanta ba
Wike ya yi zargin cewa ba a san inda Dala miliyan 308 da aka samu daga sayar da tashar wutar lantarki ta Afam a watan Disamban 2014 suka shiga ba.

Kara karanta wannan
Tinubu ya nemi izinin sake karɓo bashi kala 2 da ya kai kusan N30trn daga ƙasashen waje
Ministan ya ce ya kafa kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a George Omereji, wanda ya samu Amaechi da laifi.
Ya ƙara da cewa Amaechi ya ƙalubalanci rahoton har zuwa Kotun Ƙoli, amma ya sha kaye.

Source: Twitter
Wike ya tambayi inda aka kai Dala miliyan 308 ɗin, da Dala miliyan 49 da aka ware wa asibitin Justice Karibi-Whyte, da Naira biliyan 68 na aikin jirgin ƙasa na cikin gari, da kuma Dala miliyan 10 na aikin feshin maganin kashe ƙwari.
Ya yi zargin cewa irin waɗannan bayanai sun isa su hana tsohon gwamnan jihar Rivers neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa.
Ministan ya kuma shawarci al’ummar jihar da kada su damƙa makomarsu ta siyasa a hannun mutanen da yake kira ’yan caca a siyasa.
Wike ya caccaki Peter Obi
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai rowa, yana mai cewa bai cancanci shugabancin Najeriya ba.
Ya bayyana Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na kafafen sada zumunta, yana mai cewa shahara a intanet ba ta maye gurbin ƙwarewa da ƙarfin ikon gudanar da mulkin ƙasa.
Asali: Legit.ng
