Yan Bindiga Sun Yi Amfani da Tafiya Kamfen Tinubu, Sun Tafka Mummunan Ta'adi a Zamfara
- ’Yan bindiga sun kashe mambobin rundunar sa-kai ta JTF guda bakwai, tare da sace mazauna garin Kaura Namoda 38 a Jihar Zamfara
- Maharan sun shafe sama da sa’o’i uku a garin, bayan sun bi hanyar da ta ratsa kusa da kogi domin kauce wa shingayen tsaro
- Ana zargin cewa tafiyar jami’an tsaro zuwa Kaduna domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu ya taimaka wa ’yan bindigar kai harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe dakarun rundunar sa-kai ta JTF guda bakwai tare da yin garkuwa da mazauna garin Kaura Namoda 38 a wani harin da suka kai da tsakar dare a Jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shafe sama da sa’o’i uku suna cin karensu ba babbaka kafin daga bisani su janye.

Source: Original
Yadda yan bindiga suka kai harin
A rahoton Leadership, an ce maharan sun shiga garin ne ta wata hanya da ta ratsa kusa da kogi da sanyin safiyar ranar Asabar, inda suka kai farmaki a yankunan Kofar Zurmi da Old Market.
Shugaban Karamar Hukumar Kaura Namoda, Hon. Munnir Haidara, ya tabbatar da kashe dakaraun JTF bakwai, wadda aka kafa domin taimaka wa al’umma wajen kare kansu daga hare-hare.
Haidara ya ce ƙaramar hukumar ta ɗauki mazauna yankin aiki a rundunar tare da samar musu da makamai domin kare al’ummominsu.
Ya ƙara da cewa wasu mambobin rundunar da suka jikkata a harin na samun kulawa a asibitoci.
“Ba mu da ainihin adadin mutanen da aka yi garkuwa da su a harin jiya ba, har yanzu muna tattara bayanai, amma muna fatan samun cikakken adadin tsakanin yanzu zuwa yammacin yau,” in ji shi.
Yan JTF na kokarin bada tsaro

Kara karanta wannan
Kotu ta amince da bukatar matashin da ake zargi da taɓa mutuncin gwamna a Facebook
Wani mazaunin garin, Bello Lauwali, ya ce ’yan bindigar sun yi amfani da wata hanya ta daban da ke kusa da kogi domin kauce wa shingayen tsaron da ’yan sa-kai suka kafa a kewayen garin.
A cewar Lauwali, ’yan sa-kai kan kafa matsugunan tsaro a wajen garin, inda suke gina shingayen kariya da laka domin hana hare-hare.
Ya ce wasu daga cikinsu kan ci gaba da sintiri har zuwa misalin ƙarfe 3:00 na dare, inda a wasu lokuta suke harba bindiga domin gargaɗin ƙungiyoyin masu makamai da kada su shigo garin.
Ya ce maharan sun tare hanyoyin shiga da fita daga garin yayin da suke musayar wuta na tsawon lokaci da mambobin rundunar JTF ta farar hula.
Hakan ya sa sauran jami’an tsaro suka kasa samun damar shiga yankin cikin sauƙi saboda fargabar fadawa tarkon kwanton ɓauna.
Ana zargin jami'an tsaro sun tafi Kaduna
Wani mazaunin garin, Zayyanu Usman, ya yi zargin cewa tafiyar jami’an tsaro da ’yan sa-kai zuwa Jihar Kaduna domin halartar ƙaddamar dakamfen Shugaba Bola Tinubu ta taimaka wajen barin garin cikin haɗari.
“An kwashe kusan dukkan jami'an hukumomin tsaro, har da ’yan sa-kai, zuwa Kaduna domin gangamin yaƙin neman zaɓen. Waɗanda aka bari a baya galibi yara ne, kuma ’yan bindigar sun yi amfani da wannan dama suka kai wa garin hari,” in ji shi.

Kara karanta wannan
'Yan daba sun farmaki ayarin ɗan takarar jam'iyyar su Kwankwaso, an kashe mutum 1
Sai dai shugaban karamar hukumar Kaura Namoda ya yi watsi da wannan zargi, inda ya nace cewa waɗanda suka tafi Kaduna magoya bayan siyasa ne da masu ruwa da tsaki, ba jami’an tsaro ba.
Haidara ya tambayi dalilin da zai sa su janye jami’an da ke da alhakin kare mazauna yankin domin halartar taron siyasa.
Kun ji cewa an kashe wani fitaccen jagoran ’yan bindiga, Kachalla Mu’azu, da wasu ’yan ƙungiyarsa shida a wani artabu tsakanin ƙungiyoyi yan ta'adda a Zamfara.
Kachalla Mu’azu da mutanensa suna dawowa ne daga Kasuwar Yankara lokacin da mambobin wata dabar ’yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna a kan hanyar da suke bi.
Asali: Legit.ng
