An Kama Wanda Ya Boye Makamai a Buhu Yana Yawo da Su a Arewacin Najeriya

An Kama Wanda Ya Boye Makamai a Buhu Yana Yawo da Su a Arewacin Najeriya

  • Dakarun Sojojin Najeriya sun cafke wani mutum da ake zargin yana safarar harsasai ga ’yan bindiga, bayan sun gano harsasai 300 a cikin buhun wake
  • An kama mutumin mai suna Umaru Muhammad, mai shekaru 47, a wani samame da aka gudanar da haɗin gwiwar jami’an sa-kai a jihar Kogi
  • Dakarun sojojin sun ce harsasan na kan hanyarsu ta zuwa hannun wasu mutane biyu da ake zargi suna da alaƙa da safarar makamai a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi – Dakarun Sojojin Najeriya sun kama wani mutum da ake zargin dillalin harsasai ne, bayan sun gano harsasai 300 da ya ɓoye a cikin buhun wake a wani samame da suka gudanar a jihar Kogi.

Sojojin sun ce cafke mutumin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da suke yi na katse hanyoyin safarar makamai da sauran kayayyakin da ke taimaka wa ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Kara karanta wannan

An tona asirin Amurka kan makaman da ta kawo harin Sokoto da su a 2025

Wanda sojoji suka kama a Kogi
Wanda sojoji suka kama bisa zargin safarar makamai a Kogi. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Yadda aka kama wanda ake zargin

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojojin, Kanal Appolonia Anele, ta fitar a Facebook a ranar 18 ga Nuwamba, 2026, ta ce an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ranar Talata, 17 ga Nuwamba.

An kama shi ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda dakarun Atsawa Blocking Force suka haɗa kai da jami’an sa-kai wajen gudanar da aikin.

An bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Umaru Muhammad, mai shekaru 47, mazaunin ƙauyen Ashe.

Sojoji sun gano harsasai 300

A yayin binciken da sojojin suka gudanar, sun gano harsasai 300 da aka ɓoye a cikin buhun wake domin ɓoye manufar safararsu.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa ana zargin an shirya kai harsasan ga wasu mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gimba da Dare, waɗanda ake cewa mazauna ƙauyen Gori ne da ke yankin da ke kusa da kogin Neja, a Lokoja ta jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya fara garkuwa da mutane a Amurka, 'yan sanda na neman shi

Wasu sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Sanarwar ta ce an bayyana mutanen biyu a matsayin jami’an sa-kai na yankin, lamarin da ya jawo damuwa kan yiwuwar masu aikata laifuka na kutsawa cikin tsarin tsaron al’umma tare da amfani da shi wajen safarar makamai.

Sai dai Punch ta wallafa cewa rundunar ta jaddada cewa waɗannan bayanai na cikin bincike, kuma ba a tabbatar da zargin ba.

Amurka na taimaki Najeriya

A wani labarin, mun rahoto cewa Ministan Tsaro ya bayyana cewa sojojin Najeriya na samun bayanan sirri da hotunan tauraron ɗan adam daga Amurka domin gano tare da kai hare-hare kan shugabannin ’yan ta’adda.

Ministan ya ce dakarun sojoji sun kashe wasu shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda a hare-haren da suka gudanar a yankunan Arewa.

Ya ƙara da cewa Najeriya da Amurka na faɗaɗa haɗin gwiwarsu ta fuskar tsaro domin yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng