Taimakon da Gwamnatin Tinubu Ta Nema Kan Shirin Yan Sanda Jihohi a Najeriya

Taimakon da Gwamnatin Tinubu Ta Nema Kan Shirin Yan Sanda Jihohi a Najeriya

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci kamfanoni masu zaman kansu su tsara yadda za a samar da kuɗaɗen kafa da gudanar da ’yan sandan jihohi
  • Femi Gbajabiamila ya ce rashin tsaro na jawo asarar jarin ’yan kasuwa, tare da hana faɗaɗa masana’antu da kuma durƙusar da damar bunƙasa tattalin arziki
  • Ya gargaɗi cewa dole jihohi su tabbatar da ɗorewar kuɗaɗen biyan albashi, horo da kula da kayan aiki, tare da kare ’yan sanda daga siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta nemi taimakon kamfanoni masu zaman kansu yayin da ake shirin kafa yan sanda jihohi.

Gwamnatin ta buƙaci kamfanonin da su tsara hanyoyin samar da kuɗaɗe da aiwatar da shirin kafa ’yan sandan jihohi.

Gwamnatin Tinubu ta shirya kan kafa yan sandan jihohi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Femi Gbajabiamila, wanda kuma yake jagorantar kwamitin shugaban ƙasa kan dokar ’yan sanda ta ƙasa, ne ya yi wannan kira yayin wani zama a taron tattalin arzikin Najeriya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Kalubalen gwamnati ga kamfanoni, yan kasuwa

Gbajabiamila ya ƙalubalanci Ƙungiyar Tattalin Arzikin Najeriya (NESG), ƙungiyoyin ’yan kasuwa da hukumomin kasuwanci da su gabatar da hanyoyin samar da kuɗaɗe da gudanar da ’yan sandan jihohi cikin gaskiya da riƙon amana.

Ya ce ’yan kasuwa suna da muhimmiyar rawa wajen nasarar wannan garambawul, yana mai cewa rashin tsaro ya sa aka yi watsi da wasu jarin kasuwanci, aka jinkirta faɗaɗa masana’antu, sannan aka rasa damammakin tattalin arziki.

Gbajabiamila ya bayyana cewa ƙudurin Shugaba Bola Tinubu na kafa ’yan sandan jihohi wata dama ce ga ’yan kasuwa su taimaka wajen gina hukumomin tsaro da za su tallafa wa bunƙasar tattalin arziki.

Ya buƙaci NESG ta ci gaba da tattaunawar bayan taron, ta hanyar tuntuɓar gwamnatocin jihohi da ’yan majalisa domin tsara yadda za a samar da kuɗaɗe da aiwatar da shirin.

Gbajabiamila ya ce:

“Ku gabatar da tsare-tsaren gudummawar da ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu zai bayar wajen samar da kuɗaɗe da aiwatar da ’yan sandan jihohi, tare da shawarwarin haɗin gwiwa masu amfani da za a gudanar cikin riƙon amana.”

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

An shirya kafa yan sandan jihohi a Najeriya
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu da Bola Tinubu. Hoto: Nigeria Police Force, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Gargadin gwamnati kan shirin yan sandan jihohi

Sai dai ya gargaɗi cewa dole ne a tabbatar da gaskiya da bayyana yadda ake gudanar da haɗin gwiwar, ba tare da tauye ’yancin ’yan sanda ba.

Shugaban ma’aikatan fadar ya ce jihohin da ke son kafa nasu rundunonin ’yan sanda dole ne su nuna cewa suna da ƙarfin kuɗi da tsarin gudanarwa da zai ba su damar ɗaukar nauyin ayyukan rundunonin.

Ya bayyana cewa samar da motoci, kayan sawa da sauran kayan aiki a farkon kafa rundunar ba zai wadatar ba, idan babu tsayayyen tsarin biyan albashi, horar da jami’ai da kula da kayan aiki.

Ya yi gargaɗin cewa rashin biyan jami’an ’yan sanda albashi a kan lokaci na iya sa su shiga matsin lamba daga masu buƙatun kansu, ko kuma su amince da buƙatun da suka saɓa wa doka.

Gbajabiamila ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa rundunar ’yan sandan tarayya za ta ci gaba da aiki a jihohin da ba su da isasshen kuɗi ko tsarin hukumomi da zai ba su damar kafa nasu rundunonin.

Kara karanta wannan

IPOB: Kungiyar 'yan ta'adda ta yi magana kan alaka da APC a 2027

Yan sandan jihohi: An bukaci daukar matasa aiki

Mun ba ku labarin cewa gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya ce Najeriya na buƙatar ƙarin jami’an tsaro 554,353 domin samar da isassun ma’aikata a tsarin ’yan sandan jihohi.

Ya buƙaci kafa Asusun Fara Aiki na ’Yan Sandan Jihohi saboda kada bambancin ƙarfin kuɗin jihohi ya kawo cikas ga tsarin.

Abiodun ya ce muhawarar yanzu ba ita ce ko Najeriya na buƙatar ’yan sandan jihohi ba, illa yadda za a kafa tsarin cikin gaggawa kuma mai ɗorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.