Ana Neman Yafe wa 'Yan Najeriya Bashin Gwamnati har Naira Tiriliyan 1

Ana Neman Yafe wa 'Yan Najeriya Bashin Gwamnati har Naira Tiriliyan 1

  • An samu sabani a Majalisar Wakilai kan bukatar soke bashin Naira tiriliyan 1 da manoma suka karba karkashin shirye-shiryen tallafin noma na gwamnati
  • Wasu ‘yan majalisar na ganin ya kamata a yafewa manoman da matsalolin tsaro da sauyin yanayi suka jefa cikin matsin tattalin arziki
  • Sai dai wasu sun bukaci a gudanar da bincike domin gano wadanda suka karkatar da kudin bashin zuwa wasu harkokin da ba su shafi noma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCt, Abuja – Wata bukatar soke basussukan da manoma suka karba karkashin shirye-shiryen tallafin noma na gwamnatin tarayya ta jawo sabani tsakanin ‘yan majalisar wakilai.

Dan majalisa mai wakiltar Yamaltu/Deba a jihar Gombe, Inuwa Garba, ne ya gabatar da kudirin, inda ya bukaci a yafewa manoma basussukan da suka kasa biya sakamakon matsalolin da suka shafi harkokin noma a kasar.

Kara karanta wannan

'An jikkata mutane da dama a harin da aka kai wa Kwankwaso a Kano,' Obi

Manoma a hanyar gona
Wasu manoma na tafiya a gona. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa wasu ‘yan majalisar sun nuna rashin amincewa da soke bashin gaba daya, inda suka bukaci a fara gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden.

Dalilan neman a yafe bashin

Da yake gabatar da kudirin, Inuwa Garba ya ce matsalolin tsaro, ‘yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya, ambaliyar ruwa, fari da sauyin yanayi sun yi wa harkokin noma illa sosai.

Ya bayyana cewa wadannan matsaloli sun jawo asarar amfanin gona da jarin manoma, tare da rage kudin shigar da suke samu daga gonakinsu.

Hon. Garba ya ce da dama daga cikin manoman da suka karbi bashin gwamnati sun kasa biya ne ba wai don ba sa son yin hakan ba, sai dai saboda matsalolin da suka gagara shawo kansu.

Ya kara da cewa ci gaba da karbar bashi tare da kudin ruwa da tarar jinkiri na iya kara jefa manoman cikin talauci, har ma a kwace musu kadarorinsu.

Kara karanta wannan

Dalilan da ake gani za su iya sa Atiku ya yi nasara a kan Tinubu a 2027

Salam ya ki yarda da kudirin

Sai dai dan majalisa mai wakiltar Ede South/Ede North/Ejigbo/Egbedore a jihar Osun, Bamidele Salam, ya yi adawa da soke bashin gaba daya.

Salam ya ce rahoton babban mai binciken kudi na tarayya da ke gaban majalisar ya kunshi bayanan da ke nuna cewa wasu daga cikin wadanda suka karbi bashin noma sun karkatar da kudaden.

Ya yi zargin cewa wasu mutane sun karbi basussukan da suka kai sama da Naira tiriliyan 1, amma suka yi amfani da kudin wajen harkokin kasuwanci da zuba jari na kashin kansu.

A cewarsa, wasu daga cikin wadanda suka karbi bashin ta hannun Babban Bankin Najeriya da bankunan kasuwanci sun karkatar da kudin wajen sayen gidaje da filaye a Abuja, Legas har ma da Dubai.

Ra'ayin wasu ‘yan majalisa

Shi ma dan majalisa daga jihar Ogun, Isiaka Ibrahim, ya goyi bayan matsayar Salam, inda ya yi zargin cewa wasu mutane sun karbi bashin gwamnati amma suka karkatar da kudaden zuwa bukatunsu na kashin kai, har da yin karin aure.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fitar da sabon tsarin tsaro da zai kawo zaman lafiya a shekara 5

Sai dai ya amince cewa gudanar da cikakken bincike zai taimaka wajen gano manoman da matsalolin tattalin arziki suka hana su biyan basussukansu.

Majalisar wakilai a Abuja
'Yan majalisar wakilai yayin tattaunawa a Abuja. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: UGC

Haka kuma, Paul Kalejaiye, dan majalisa daga jihar Legas karkashin jam’iyyar APC, ya bukaci majalisar ta yi taka-tsantsan kafin yanke hukunci kan batun.

Tinubu zai raba taki a Najeriya

A wani labarin, mun rahoto cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki su gaggauta samar da buhunan taki sama da miliyan 3 domin tallafa wa manoma.

Gwamnatin tarayya ta shirya sayen takin da kamfanonin cikin gida suka samar domin sayar wa manoma kan farashi mai sauki, a wani mataki na rage musu nauyin kudin noma.

Shettima ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci wajen rabon takin, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng