Atiku Ya Yi wa Tinubu Zafafan Tambayoyi kan Ciwo Bashin $20bn da £1bn

Atiku Ya Yi wa Tinubu Zafafan Tambayoyi kan Ciwo Bashin $20bn da £1bn

  • Atiku Abubakar, da jam’iyyar ADC sun yi watsi da sabon shirin Shugaba Bola Tinubu na karɓar bashin dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045 daga ƙasashen waje
  • Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da neman karɓar basussuka ba tare da bayyana takamaiman ayyukan da za a kashe kuɗin a kansu ba, yana mai cewa hakan bai dace ba
  • ADC ta bayyana shirin a matsayin wanda bai dace ba, tare da buƙatar Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta ƙi amincewa da bashin har sai gwamnati ta yi cikakken bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Dan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar da jam’iyyar sun yi Allah-wadai da sabon shirin Shugaba Bola Tinubu na neman amincewar karɓar bashin dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta kafa tarihi bayan kammala sayar da hannayen jari

Sun bayyana shirin a matsayin wanda ba shi da kyakkyawan tsari, yana kuma iya zama barazana ga makomar tattalin arzikin Najeriya.

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Atiku Abubakar a hagu da Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Facebook

Leadership ta wallafa cewa Atiku ya ce wannan buƙata ta shugaban ƙasa ta tabbatar da gargaɗin da ya yi a ranar 12 ga Oktoba, inda ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na shirin karɓar bashin da ya kai dala biliyan 20.

Atiku ya soki Tinubu kan bashi

A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce tun da farko ya gargaɗi ’yan Najeriya kan shirin karɓar bashin da ake zargin zai danganci aikin babbar hanyar Legas zuwa Kalaba ta gabar teku.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda shugaban ƙasa ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓar basussukan daga ƙasashen waje, ba tare da bayyana takamaiman ayyukan da za a gudanar da kuɗin a kansu ba.

Atiku ya ce:

“A ranar 12 ga Oktoba, na gargaɗi ’yan Najeriya cewa ana zargin Shugaba Tinubu na shirin karɓar bashin da ya kai dala biliyan 20 dangane da babbar hanyar Legas zuwa Kalaba.

Kara karanta wannan

"Bai cancanta ba," An tono abin da zai iya zama matsala ga abokin takarar Atiku a 2027

"Na nemi ya tabbatar ko ya musanta shirin, tare da wallafa bayanan kuɗin. Bai yi ɗaya daga cikin waɗannan ba. Yanzu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da bashin dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045. Wannan ya tabbatar da gargaɗina.”

Ya ce duk da cewa gwamnatin ta ambaci wasu manyan fannoni da za a iya amfani da kuɗin a kansu, ba ta bayar da cikakken bayani kan kowane aiki, kuɗin da zai ci, wurin da za a gudanar da shi ko kamfanonin da za su yi aikin ba.

Bolaji Abdullahi na ADC
Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

ADC ta soki Bola Tinubu

A wata sanarwa dabam, kwamitin din kamfen ɗin ADC ya yi Allah-wadai da shirin karɓar bashin, tana mai bayyana shi a matsayin wani mataki marar kyau da zai iya jefa Najeriya cikin wani yanayi na dogaro da ƙasashen waje wajen tafiyar da tattalin arzikinta.

Jam’iyyar ta ce wannan na zuwa ne a lokacin da ’yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, ƙarin haraji da kuma cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.

ADC ta nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da neman manyan basussuka ba tare da bayyana yadda aka yi amfani da tsofaffin basussuka da kuɗin da aka samu bayan cire tallafin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Tallafin mai: ADC ta sake albishir ga Ƴan Najeriya kan shirin Atiku bayan hawa mulki

Daraktan yaɗa labarai na kwamitin kamfen ɗin ADC, Kola Ologbondiyan, ya ce:

“Wane aiki ne Shugaba Tinubu yake son ya yi da duk waɗannan kuɗin? Ina hanyoyi, wutar lantarki, asibitoci, ayyukan yi da muhimman abubuwan more rayuwa da ya kamata su tabbatar da dalilin ci gaba da tara basussuka? ’Yan Najeriya sun cancanci samun amsoshi.”

Tinubu zai kawo sabuwar doka

A wani labari, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya na duba yiwuwar samar da wata doka da za ta kare sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya daga soke su idan wata sabuwar gwamnati ta karɓi mulki.

Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin taron koli kan tattalin arzikin Najeriya karo na 32 da aka gudanar a Abuja.

Oyedele ya ce gwamnati na neman cimma matsaya ta ƙasa baki ɗaya kan tsarin manufofin tattalin arziki da za a iya kafa wa doka, domin jagorantar matakan da gwamnatoci masu zuwa su yi aiki da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng