Sojoji Sun Kwato Mutane 70, Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga da Ya Addabi Mutane a Arewa
- Rundunar sojin Najeriya ta ƙara ƙaimi a yankuna daban-daban na Arewacin ƙasar domin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa
- Sojoji sun kuɓutar da mutane sama da 70 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina, Neja da Kano, tare da kama wani fitaccen jagoran ’yan ta’adda
- Dakarun sun kuma ƙwato Naira miliyan 10 da ake zargin kuɗin fansa ne, tare da kwato makamai da alburusai a wasu samame
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rundunar sojin Najeriya ta ƙara tsaurara ayyukan yaƙi da ta’addanci a dukkan wuraren da take gudanar da ayyukanta a Arewacin ƙasar, da nufin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.
Wannan na zuwa ne yayin da dakarun sojoji suka kuɓutar da mutane sama da 70 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wani fitaccen jagoran ’yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo.

Kara karanta wannan
Kotu ta yi hukunci kan wani matashi da ya yi barazanar sakin hotunan tsiraicin Gwamna Abba

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya sake jaddada aniyarsa ta samar da yanayin zaman lafiya da tsaro a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana cewa dakarun soji na matsa wa ’yan ta’adda lamba ta kowane ɓangare ta hanyar ci gaba da kai musu hare-hare.
Da yake yi wa ’yan Najeriya bayani kan matakan dawo da zaman lafiya da rundunar ke ɗauka, daraktan yaɗa labaraina hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar Michael Onoja, ya ce an gudanar da samamen a wurare daban-daban na ƙasar.
Yadda sojoji suka kubutar da mutane
A jihar Katsina, bayan samun kiran neman agaji a ranar 16 ga Oktoba, sojoji sun yi artabu da ’yan ta’adda da suka yi garkuwa da mazauna ƙauyen Gamji, da ke ƙaramar hukumar Sabuwa.
Rahotanni sun ce sojojin sun yi galaba a kan maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Haka kuma, a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja, sojoji sun kuɓutar da mutane 29 da suka tsere zuwa cikin daji bayan wasu ’yan ta’adda da ke kan babura bakwai sun yi ƙoƙarin yin garkuwa da manoma a ƙauyen Magaji Mai Kadarko.
An ƙwato kuɗin fansa a Kano
A wani samame da aka gudanar a jihar Kano, sojoji sun bi sawun masu garkuwa da mutane daga ƙauyen Fanyabo da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada zuwa yankin Yan Taburmi a dajin Falgore.
A yayin samamen, sojojin sun kashe mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin tare da kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi.
Dakarun sun kuma ƙwato naira miliyan 10 da ake zargin kuɗin fansa ne da iyalan wanda aka sace suka biya.
Bayan haka, an miƙa kuɗin da kuma wanda aka kuɓutar ga iyalansa, a gaban shugabannin al’umma da jami’an ’yan sanda.

Source: Facebook
An kama jagoran ’yan ta’adda a Neja
A wani gagarumin samame da aka gudanar a garin Mokwa da ke jihar Neja, sojoji sun kama wani fitaccen jagoran ’yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo tare da wani da ake zargin abokin aikinsa ne.
An kama mutanen ne a ranar 18 ga Oktoba, inda sojoji suka ƙwato wayoyin hannu guda huɗu da kuma wasu kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba.
Sojoji sun kashe yan ta'adda 103
Kun ji cewa Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta kashe ’yan ta’adda 103 a hare-haren sama bakwai da ta kai tsakanin 10 zuwa 18 ga Oktoba 2026
Hare-haren sun lalata wuraren ajiyar kayayyaki da cibiyoyin samar da kayan aiki na kungiyar ISWAP a jihohin Borno da Adamawa.
Asali: Legit.ng

