Musulunci zai Zama Addini Mafi Yawan Mabiya a Duniya, zai Zarce Kiristanci

Musulunci zai Zama Addini Mafi Yawan Mabiya a Duniya, zai Zarce Kiristanci

  • Wani sabon bincike ya nuna cewa Musulunci na iya zama addini mafi yawan mabiya a duniya, inda zai zarce Kiristanci nan da shekarar 2035
  • Cibiyar bincike ta Pew ta ce yawan Musulmi zai ci gaba da ƙaruwa cikin sauri fiye da na Kiristoci a shekaru masu zuwa
  • Binciken ya yi nazari kan ƙasashe da yankuna 201, inda ya yi hasashen sauyin yawan mabiya addinai daban-daban daga 2020 zuwa 2070

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani sabon bincike da cibiyar Pew ta gudanar ya nuna cewa Musulunci na dab da zama addini mafi yawan mabiya a duniya, inda zai iya maye gurbin Kiristanci a matsayi na farko nan da shekarar 2035.

A rahoton da cibiyar ta fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa yawan Musulmi da Kiristoci zai ci gaba da ƙaruwa a duniya cikin shekaru masu zuwa, amma Musulmi za su ƙaru cikin sauri fiye da Kiristoci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano dabarun 'yan kasuwa, za a kawo karshen kauce wa biyan haraji

Dakin Ka'aba a Makkah
Musulmi na dawafi a dakin Ka'aba. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta rahoto cewa binciken ya ƙunshi ƙasashe da yankuna 201, waɗanda suka kai kashi 99.98 cikin 100 na al’ummar duniya, inda aka yi hasashen sauyin yawan mabiya addinai bakwai daga shekarar 2020 zuwa 2070.

Musulmi za su karu a duniya

Rahoton ya bayyana cewa yawan haihuwa na daga cikin manyan dalilan da ke sa Musulunci zama addinin da ke ƙaruwa cikin sauri a duniya.

Binciken ya nuna cewa kowace mace Musulma tana haihuwar yara 3, yayin da kowace mace Kirista ke haihuwar yara 2

Masu binciken sun bayyana cewa ana buƙatar mace ta haifi yara kusan 2 domin al’umma ta iya maye gurbin kanta daga wannan tsara zuwa wata.

Pew ta yi hasashen cewa Musulmi za su iya ƙaruwa da mutane biliyan 1.6 sakamakon haihuwa da sauyin yawan jama’a, yayin da Kiristoci za su ƙaru da miliyan 792.

Mutanen da ke barin addini

Binciken ya kuma nuna cewa Musulunci zai fuskanci raguwar mabiya kaɗan sakamakon sauya addini idan aka kwatanta da Kiristanci.

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Rahoton ya ce bambancin yawan mutanen da za su shiga Musulunci da waɗanda za su fita daga cikinsa zai haifar da raguwar mutum miliyan 8 a lokacin hasashen.

A ɓangaren Kiristanci kuwa, ana sa ran bambancin zai haifar da raguwar mabiya miliyan 105.

Masu binciken sun bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda za su bar Kiristanci na iya komawa matsayin marasa alaƙa da wani addini, ciki har da waɗanda ba su yarda da samuwar Allah ba ko kuma ba su da tabbataccen matsayi kan hakan.

Sai dai rahoton ya jaddada cewa ƙarin yawan Musulmi ba zai kasance sakamakon yawan Kiristocin da ke karɓar Musulunci ba, domin ana sa ran yawan Musulmin da za su koma Kiristanci zai ɗan fi na Kiristocin da za su karɓi Musulunci.

Pakistan za ta zarce Indonesia

Reueter ta wallafa cewa Pew ta bayyana cewa mafi yawan ƙarin Musulmi daga 2020 zuwa 2070 zai faru ne a ƙasashen da Musulmi suka riga suka fi yawa.

Rahoton ya yi hasashen cewa nan da 2070, Musulmi za su kai kashi 95 cikin 100 na al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya fara garkuwa da mutane a Amurka, 'yan sanda na neman shi

Haka kuma, a yankin Asiya da tekun Pasifik, ana sa ran Musulmi za su zarce mutanen da ba su da alaƙa da wani addini.

Musulmai na sallah a masallaci.
Al'ummar Musulmi suna sallah a masallaci. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Binciken ya nuna cewa a shekarar 2020, Musulmi sun fi yawa a ƙasashe 53. Ana sa ran ƙarin Musulmi biliyan 1.2 za su zauna a waɗannan ƙasashe nan da 2070, wanda zai wakilci kashi 74 cikin 100 na dukkan ƙarin Musulmin duniya.

Misali, ana hasashen yawan Musulmin Pakistan zai ninka daga miliyan 227 a shekarar 2020 zuwa miliyan 461 nan da 2070. Hakan zai sa Pakistan ta zama ƙasar da ta fi kowace yawan Musulmi, inda za ta zarce Indonesia.

A ɓangaren Kiristoci kuwa, ana sa ran mafi yawan ƙarin mabiya zai faru ne a ƙasashe 120 da Kiristoci suka riga suka fi yawa, inda za a samu ƙarin mutane miliyan 630, kwatankwacin kashi 92 cikin 100 na dukkan ƙarin Kiristocin duniya.

Mutane masu rayuwa a daji

A wani labarin, mun rahoto cewa an gano wasu ’yan wata ƙabila da ta keɓe kanta daga sauran al’umma a cikin dajin Amazon da ke ƙasar Brazil.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Ƙungiyar kare haƙƙin ’yan asalin ƙasa ta Survival International ta bayyana cewa masu sare itatuwa, mafarauta da masu kiwon shanu na ƙara kutsawa yankunan da ƙabilar ke zaune, lamarin da ke jefa rayuwarsu cikin haɗari.

Hukumar kula da ’yan asalin ƙasar Brazil ta ce ta fara ɗaukar matakan kare lafiyar mutanen bayan bayyanar hotunan ganawar da aka yi da su, musamman domin rage haɗarin kamuwa da cututtuka sakamakon hulɗa da mutanen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng