Da Gaske Majalisar Amurka Ta Zabi Wanada Take Goyon Baya a Zaben 2027? Bayanai Sun Fito

Da Gaske Majalisar Amurka Ta Zabi Wanada Take Goyon Baya a Zaben 2027? Bayanai Sun Fito

  • Wani kamfanin a Amurka ya musanta ikirarin cewa Majalisar Dokokin Amurka ta ayyana goyon bayanta ga Peter Obi a zaben 2027
  • Kamfanin ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC ya halarci wani taro na sirri ne, ba taron Majalisar Dokokin Amurka ba
  • Dr Von Batten ya ce babu wani daga cikin mutanen da suka bayyana a bidiyon da ke cikin kwamitin harkokin wajen Majalisar Wakilan Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Wani kamfanin masu yi wa 'yan siyasa da ƙoƙarin samun goyon baya a Amurka, Von Batten-Montague-York, L.C., ya yi karin haske kan haduwar Peter Obi da wasu yan Majalisa.

Kamfanin ya musanta ikirarin cewa Majalisar Dokokin ƙasar Amurka ta gana da Peter Obi ko kuma ta amince ta goyi bayan takararsa ta shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan Kano ya faɗawa Tinubu gaskiya kan ƙalubalen da APC za ta fuskanta a Arewa

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi tare da wasu yan Majalisar dokokin Amurka Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Hakan na kunshe a wata sanarwa da kamfanin Von Batten-Montague-York, L.C., ya wallafa a shafinsa na X domin martani kan jita-jitar da aka fara yadawa kan ziyarar Peter Obi.

Wannan bayani ya biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo a ranar Talata, wanda ya nuna Peter Obi yana jawabi ga wasu mutane da aka bayyana a matsayin 'yan majalisar dokokin Amurka.

Sai dai kamfanin ya bayyana ta bakin wakilinsa, Dr Von Batten, cewa Obi ya halarci wani taro na sirri ne, ba wata ganawa ta hukuma da Majalisar Dokokin Amurka ba.

A cikin wata sanarwa, Von Batten ya ce babu wani daga cikin mutanen da suka bayyana a bidiyon da ke cikin kwamitin harkokin wajen Majalisar Wakilan Amurka ko kuma ƙaramin kwamitinta mai kula da Afirka.

Ya kuma bayyana cewa babu wani jami'in ofishin harkokin Afirka na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da ya halarci taron.

Von Batten ya yi karin bayani

Kara karanta wannan

Abin da na jikin Tinubu suka gano wanda ya nuna Arewa na tare da shugaban ƙasa

Dr Von Batten ya ce ya san duk mutanen da suka bayyana a bidiyon, amma babu wani jami'in Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka daga ofishin harkokin Afirka a cikinsu.

Ya ce:

“Na san duk mutanen da ke cikin bidiyon, kuma babu wani jami'in ofishin harkokin Afirka na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da ya bayyana a cikinsa.
“Na gane ɗan majalisa Stutzman da 'yar majalisa Van Duyne, amma babu ɗayansu da ke cikin kwamitin harkokin wajen Majalisar Wakilan Amurka. Suna aiki ne a wasu kwamitoci da ke da alhakin kula da kasafin kuɗi da ƙananan sana'o'i.”

Kamfanin ya jaddada cewa manufar wannan ƙarin bayani ba ita ce rage muhimmancin ziyarar Obi ba, sai dai gyara rahotannin da ke nuna cewa ganawar wani taro ne na hukuma da Majalisar Dokokin Amurka.

Von Batten ya ƙara da cewa:

“Ba ina ƙoƙarin rage muhimmancin ziyarar Mista Obi ba nd, kawai ina son bayyana gaskiyar lamarin ne saboda an ambaci kamfanina a cikin rahotannin.”

Peter Obi ya tuna da jihar Kano

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi magana kan irin damarmakin da jihar Kano take da su a fannin masana'antu.

Obi ya bayyana Kano a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a ƙasar, yana mai cewa sake buɗe masana’antun da suka daina aiki zai taimaka wajen samar da ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262