Saboda Ya Je Ya Yanke Masu Wutan Gida, An Kashe Ma’aikacin Kamfanin Lantarki
- An kashe ma'aikacin kamfanin BEDC saboda ya cire wa wani gida wutar lantarki a yankin Umunede da ke jihar Delta
- Shugabannin kamfanin sun ce rikicin bashin wutar lantarki ya yi sanadiyyar mutuwar ma'aikacin mai shekaru 38 a duniya
- Kamfanin BEDC ya ce 'yan sanda sun kama mutum biyar da ake zargin suna da hannu a kisan ma'aikacin wutar lantarkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Edo - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Benin (BEDC) ya ce an kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wani ma'aikacinsa
An hallaka wannan ma’aikaci mai suna Oscar Eze ne a garin Umunede da ke Jihar Delta, bayan ya yanke wa wani gida wutar lantarki.

Source: Twitter
Yanke wuta ya sa an hallaka ma'aikacin BEDC
Mukaddashin shugaban kamfanin, Jonathan Lawani ya shaida hakan ranar Laraba yayin wani taron manema labarai in ji Premium Times.
Da yake jawabi a hedikwatar kamfanin a Benin, Lawani ya ce an kashe marigayin ne wajen gudanar da aikin da kamfanin nasu ya tura shi.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan ma'aikacin ya cire wa wani gida lantarki saboda bashin kudin wutar da ya kai kusan N300,000.
Mutane sun je gida sun kashe ma'aikacin wuta
A cewarsa, wasu mutane sun bi sawun Eze har zuwa wani gida a cikin garin, inda suka daba masa wuka sau da dama har ya mutu a wurin.
Lawani ya ce cire wutar da marigayin mai shekaru 38 ya yi daidai da dokokin hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya (NERC).
Ya ce cire wuta ne kawai NERC ta amince da shi a matsayin matakin tilasta wa mutanen da suka ki biyan kudin wutar lantarki su biya bashinsu.
Kamfanin BEDC ya soki kashe masa ma'aikaci
Daily Trust ta rahoto shugaban kamfanin ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai cewa bai kamata a kai wa ma'aikatan wuta hari saboda aikinsu ba.

Kara karanta wannan
Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku
Ya ce shugabannin kamfanin sun kai ziyara ofishin AIG da DPO na ‘yan sandan Umunede da kuma gidan da aka kashe ma'aikacin a ranar Talata.
Lawani ya kara da cewa an kama mutum biyar da ake zargi, yayin da wasu suka tsere ana neman su.
Marigayin ya bar yaro da tsohuwarsa
Shugaban kamfanin ya bayyana cewa marigayin ya bar yaro guda daga aurensa na farko, da matarsa da ya aura watanni hudu da suka gabata.
Oscar Eze ya mutu ya bar kuma tsohuwar mahaifiyarsa. Don haka aka yi kira ga hukuma su biya hakki kuma su ba ma’aikatan kamfanin kariya.
An yi kira ga gwamnatin Jihar Delta da ta samar da isasshen tsaro ga ma'aikatan kamfanin domin ci gaba da kai masu hari na iya taba ayyukan BEDC.

Source: Getty Images
Shugabannin APC suna gadon asibiti
Ana da labari cewa hatsarin ya rutsa da mutane bakwai ciki har da shugabannin APC a Gombe, har wani mai babur ya rasu sakamakon raunuka.
Shugaban APC na Gombe Mohammed Dantata Ndus da daraktan yakin zaben Sa’adu Hassan sun yi hadarin ne a hanyar zuwa taro a Balanga.
Hatsarin ya faru a ranar Talata 17 ga Nuwamba 2026 lokacin da Jamilu Gwamna yake yawon kamfe.
Asali: Legit.ng
