Tallafin 50,000: Hanyoyi 6 da Masu MoMo Za Su Bi domin Duba ko Sun Cancanta
- Gwamnatin tarayya ta samar da lambar USSD da masu amfani da MoMo PSB za su duba cancantarsu domin karɓar tallafin N50,000
- Tallafin na NERSI yana karkashin ma’aikatar jin ƙai da rage talauci, kuma an tanade shi ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi
- Gwamnati ta yi gargaɗin cewa babu kuɗin rajista ko na kunna asusu da ake buƙata kafin karɓar tallafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta samar da wata hanya da masu amfani da MoMo Payment Service Bank (PSB) za su duba cancantarsu da karɓar tallafin N50,000.
Wannan tallafi na cikin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI), wanda aka tsara domin taimaka wa talakawa da iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

Source: UGC
Ma’aikatar Jin Ƙai da Rage Talauci ta Tarayya ce ke kula da shirin, wanda manufarsa ita ce rage matsin tattalin arziki sakamakon tsadar rayuwa, cewar Leadership.
MoMo PSB na cikin kamfanonin biyan kuɗi guda biyar da gwamnatin tarayya ta amince da su domin raba tallafin ga waɗanda suka cancanta.
A cewar shafin NERSI na gwamnati, masu amfani da MoMo za su iya amfani da lambar USSD domin bincika cancantarsu ba tare da amfani da intanet ba.
Yadda za a duba cancanta da karɓar tallafi
Masu amfani da MoMo PSB za su iya bin matakan da ke ƙasa domin bincika ko gwamnatin tarayya ta zaɓe su cikin waɗanda za su amfana.
1. Danna lambar USSD: Buɗe wajen kiran waya, sannan ka danna 6710# ta amfani da lambar wayar da aka yi wa rajista.
2. Duba cancanta: Zaɓi inda aka tanada domin bincika cancantarka cikin shirin tallafin NERSI na gwamnatin tarayya.
3. Bi umarnin da aka bayar: Idan gwamnati ta zaɓe ka, sai ka bi umarnin da zai bayyana a allon wayarka.
4. Amincewa da tallafin: Tabbatar da amincewarka wajen karɓar tallafin N50,000 da gwamnatin tarayya ta ware.

Kara karanta wannan
Tallafin N50,000: Gwamnatin Tarayya ta fitar da ka'idoji 4, ta ja kunnen 'yan Najeriya
5. Karɓar kuɗin: Bayan kammala matakan, za a kunna maka walat ɗin wayarka, sannan a tura maka kuɗin tallafin.
6. Tabbatar da ciniki: Za ka samu saƙon SMS da zai tabbatar maka cewa an tura kuɗin cikin walat ɗinka.

Source: Facebook
Su waye suka cancanci tallafin N50,000?
Shirin ya shafi iyalai masu ƙaramin ƙarfi da waɗanda ke cikin mawuyacin hali a faɗin yankuna shida na Najeriya.
Sai dai samun asusun MoMo PSB ba yana nufin mutum ya cancanci tallafin kai tsaye ba, domin gwamnati ce ke tantance waɗanda za su amfana.
Haka kuma, babu wata hanyar buɗe rajista ga jama'a da mutum zai bi da kansa domin neman tallafin.
Gwamnati na raba kuɗaɗen ne a matakai daban-daban, don haka wasu waɗanda aka zaɓa na iya samun sanarwar karɓar tallafin daga baya.
Tallafin 50k: Yadda Opay ke tantance lambobi
An ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ce zabar waɗanda za su amfana da tallafin NERSI, yayin da Moniepoint da OPay ke taimakawa wajen tantance cancanta da aika kuɗin.
Ana amfani da lambobin waya wajen duba cancanta, amma mallakar asusu a banki ba ya sa mutum ya cancanci tallafin Naira 50,000 kai tsaye.
Ana biyan tallafin ne a matakai daban-daban, don haka sakamakon “Ba a zabe ka ba” yana nufin ba a zaɓi mutum a wannan matakin ba.
Asali: Legit.ng
