Yan Sanda Sun Kama Ɗan Agajin Izala kan Zargin Barazana ga Kiristoci a Bidiyo

Yan Sanda Sun Kama Ɗan Agajin Izala kan Zargin Barazana ga Kiristoci a Bidiyo

  • Rundunar ’yan sandan Zamfara ta kama wani matashi, Umar Ibrahim Gandi Maradun, kan wani bidiyo da ya yaɗu yana barazanar kashe Kiristoci
  • Kwamishinan ’yan sanda, Muhammad Bello, ya ce ana ci gaba da bincike kan zargin tunzura jama’a zuwa tashin hankali da kuma barazana
  • Rundunar ta buƙaci malamai, iyaye da al’umma su ƙarfafa zaman lafiya, haƙuri da mutunta juna, tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tantance ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta kama wani matashi bisa zargin bayyana a cikin wani bidiyo da ya yaɗu, yana rera waƙar kira ga kashe Kiristoci.

Bidiyon ya nuna wanda ake zargin sanye da kayan ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen jihar Zamfara, tare da wasu ɗalibai daga makarantun Islamiyya biyu da ke ƙaramar hukumar Maradun.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan wani matashi da ya yi barazanar sakin hotunan tsiraicin Gwamna Abba

Yan sanda sun kama matashin dan agajin Izala
Taswirar jihar Zamfara da aka cafke matashin dan agajin Izala. Hoto: Legit.
Source: Original

Matashin dan agajin Izala ya shiga hannun yan sanda

Hakan na cikin wata sanarwa ga manema labarai bayani a Gusau ranar Talata, kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Bello, ya fitar kamar yadda aka wallafa a Facebook.

Ya ce rundunar ta himmatu wajen kare dukkan mazauna jihar, ba tare da la’akari da addininsu ba.

An bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Umar Ibrahim Gandi Maradun, kungiyar JIBWIS ce ta fara kama shi kafin ta miƙa shi ga ’yan sanda domin gudanar da bincike.

A cewar ’yan sanda, bidiyon ya ƙunshi kalaman cewa:

“Ku ba mu bindigogi mu je mu kashe Kiristoci.”

Rundunar ta ce ta yi amfani da hanyoyin tattara bayanan sirri domin gano waɗanda abin ya shafa da kuma tabbatar da yanayin da aka ɗauki bidiyon.

Binciken farko ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026, lokacin da wanda ake zargin ke kan hanyarsa ta zuwa Masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib.

Kara karanta wannan

Masussuka: Shehu Sani ya faɗi 'dalilai' da ke jawo kisan malamai a Arewa

Makarantun biyu da aka danganta da bidiyon su ne Nurul Islam Islamiya da Akidatul Sahiha Islamiya, waɗanda ke ƙaramar hukumar Maradun, mai tazarar kusan kilomita 120 daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

’Yan sanda sun ce sun tuntubi shugabannin ƙungiyar JIBWIS na ƙasa da na jiha bayan bayyanar bidiyon.

Dan agajin Izala ya shiga hannun yan sanda
Kwamishinan yan sandan Zamfara, Muhammad Bello da matashin dan agajin Izala, Umar Ibrahim Gandi. Hoto: Zamfara Police Command.
Source: Facebook

Yaushe matashin ya shiga agajin Izala?

’Yan sandan sun ce matashin ya shiga ƙungiyar JIBWIS a shekarar 2025, sannan kwanan nan ya samu gurbin karatun digiri na farko a fannin sadarwa ta zamani a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara.

Bello ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace bayan kammala binciken.

Ya ce tuhumar da ake shirin yi wa matashin za ta shafi zargin tunzura jama’a zuwa tashin hankali, tayar da hankalin jama’a da kuma barazanar aikata laifi, bisa sashe na 77, 78 da 380(b) na dokar laifuffuka da ta shafi jihar Zamfara.

Sai dai ya bayyana cewa za a yi la’akari da shaidun da aka tattara da kuma dokokin da suka dace kafin yanke shawarar ƙarshe kan tuhumar.

Kara karanta wannan

Obi ya bukaci Bola Tinubu ya koma gida ya huta, ya bar maganar takarar 2027

Kwamishinan ya yi Allah-wadai da duk wani aiki da zai iya haifar da ƙiyayya tsakanin mabiya addinai, barazana ga tsaron al’umma ko kuma kawo cikas ga zaman lafiya.

Ya sake jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, da kuma tabbatar da haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki ya bai wa ’yan ƙasa, ciki har da ’yancin tunani, lamiri da addini.

Ya buƙaci shugabannin addinai, iyaye, masu kula da yara, mahukuntan makarantu da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma su ƙarfafa haƙuri, mutunta juna da ɗabi’a mai kyau, musamman tsakanin matasa.

Izala ta magantu kan bidiyon dan agaji

A baya, an ji cewa Kungiyar Izala ta Najeriya ta yi Allah wadai da bidiyon wani matashi sanye da kayan agajjinta hana fadar kalaman tunzura jama'a.

Sheikh Bala Lau ya bukaci jami’an tsaro gudanar da bincike kan bidiyon dan agajin, wanda ke ta yada wa a kafafen sada zumunta.

Mutashin da ya bayyana a bidiyon yana neman a ba su bindigogin AK-47 domin su je Enugu da Joa ranar Lahadi su kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.