Yadda Gwamnoni Za Su Jawo Jama'a a Jiki bayan Wahalar Cire Tallafin Mai

Yadda Gwamnoni Za Su Jawo Jama'a a Jiki bayan Wahalar Cire Tallafin Mai

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya zama dole domin amfanin kasa
  • Uzodimma ya ce cire tallafin ya kara wa jihohi 36 da Abuja kudaden gudanar da ayyukan more rayuwa, duk da wahalhalun da matakin ya janyo wa iyalai
  • Gwamnan ya bukaci gwamnati ta rika yi wa jama’a bayani kan manufofinta cikin gaskiya domin gina amana da fahimtar dalilan daukar matakai masu wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a ranar Laraba, ya kare matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya zama dole domin amfanin kasa duk da wahalhalun da ya janyo wa ’yan Najeriya.

Uzodimma ya ce duk da cewa cire tallafin ya kara wa iyalai da dama nauyin kashe kudi a farko, gyaran ya samar da karin kudaden da jihohi 36 da Abuja za su iya amfani da su wajen gudanar da ayyukan more rayuwa da ci gaba.

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Gwamna ya kare matakin Tinubu na cire tallafin mai
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Hope Uzodinma. Hoto: Bayo Onanuga, Hope Uzodinma.
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin magana a wajen taron Global Alliance World Public Relations Forum da aka gudanar a Abuja, cewar Punch.

Aikin da ke gaban gwamnoni

Ya ce dole ne gwamnoni su kasance a shirye su dauki matakai masu wahala tare da ci gaba da gina amincewar jama’a ta hanyar sadarwa mai gaskiya da daidaito.

Ya ce kalubalen ya fi kamari ga sabbin gwamnatoci, wadanda manufofinsu za su iya janyo wa jama’a wahala a farko kafin su fara ganin amfanin matakan da aka dauka.

Uzodimma, wanda ya yi amfani da kwarewarsa a matsayin gwamnan Imo, ya ce cire tallafin man fetur ya nuna irin wahalar aiwatar da sauye-sauyen da jama’a ba za su fahimci amfaninsu nan take ba.

Gwamnan ya ce:

“Dukkanmu mun ga hakan lokacin da aka cire tallafin man fetur. An samar da tallafin ne domin taimaka wa talakawan Najeriya, amma mafi yawan amfaninsa ya karkata ne ga masu shiga tsakani a bangaren man fetur.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin shugaban ƙasa ya yi wa gwamna Abba Kabir tayin mata

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa sun zama dole su kawo karshen tsarin tallafin saboda hakan shi ne matakin da ya dace domin moriyar kasarmu baki daya.”
Uzodinma ya ƙare matakan Tinubu
Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo. Hoto: Hope Uzodinma.
Source: UGC

Tabbas ana shan wahala - Gwamna Uzodinma

Gwamnan ya tuna cewa a baya ’yan Najeriya daga bangarori daban-daban sun yi ta kira da a cire tallafin man fetur, yana mai cewa kudaden da aka samu sun kara karfin arzikin gwamnatocin jihohi da Abuja.

Sai dai ya amince cewa iyalai da dama sun fuskanci matsaloli sakamakon karin farashin kayayyaki da ya biyo bayan cire tallafin, cewar Vanguard.

Uzodimma ya ce dole ne gwamnatoci su bayyana dalilan daukar matakai masu wahala tare da nuna yadda jama’a za su amfana daga baya.

Da yake amfani da misalin wata manufar sufuri da za a iya aiwatarwa a Owerri, ya bayyana cewa samar da motocin bas na zamani masu saukin kudin mota zai iya rage kudin sufuri ga ma’aikata, ’yan kasuwa da dalibai.

A cewarsa, wannan misali ya nuna dalilin da ya sa dole gwamnatoci su yi la’akari da bangarori daban-daban da manufofinsu za su shafa tare da tattaunawa da su domin samar da fahimtar juna da amincewa.

Kara karanta wannan

An gargaɗi jami'an tsaro kan harbin jama'a bayan yi wa Tinubu ihu a masallaci

Gwamnan ya ce:

“A matsayimmu na gwamnati, aikinmu shi ne yada alheri ga jama’a gwargwadon yadda za mu iya, tare da bayyana manufofinmu, dalilanmu da burinmu ga wadanda za su fuskanci wasu wahalhalu a kan hanya."

An shawarci yan Najeriya kan cire tallafi

An ji cewa daya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NRM, ta yi magana kan dawo da tallafin man fetur.

Ta bayyana cewa babban ƙalubalen cire tallafin shi ne tabbatar da gaskiya da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu.

Okereke ta yi kira ga gwamnati da ta karkatar da kuɗaɗen tallafin zuwa ayyukan raya ƙasa, inganta walwala da samar da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.