Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan ISWAP, an Kashe Babban Kwamanda da Wasu Mayaka

Sojoji Sun Toshe Kofofin Tsira ga 'Yan ISWAP, an Kashe Babban Kwamanda da Wasu Mayaka

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe Abu Zubiru da wasu mayaka 15 a hare-haren sama da manyan bindigogi da suka kai sansanonin ’yan ta’adda uku
  • Sojojin sun ce Abu Saleem, wanda bayanan sirri suka bayyana a matsayin gwamnan Tunbunma, ya samu munanan raunuka tare da wasu mayaka bakwai
  • Hedikwatar Operation Hadin Kai ta bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda 37 cikin sa’o’i 72 na hare-haren soji a yankin Arewa maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kashe wani babban kwamandan ’yan ta’adda mai suna Abu Zubiru.

Sojojin sun kashe kwamandan ne tare da wasu mayaka 15 a hare-haren soji da suka kai yankin Tafkin Chadi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Kakakin rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 26 ga watan Oktoban 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bazama aiki, sun dauki matakin gano makasan Sheikh Masussuka

Ya ce an gudanar da hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen yaƙi da manyan bindigogi, inda aka kai farmaki kan wasu sansanonin ’yan ta’adda uku da ake zargi da kasancewa a yankin Tunbunma, da ke kudancin Tafkin Chadi.

Yadda sojoji suka kai harin

A cewar Goni, an gudanar da aikin sojin tsakanin ƙarfe 1:00 da 2:00 na dare a ranar 26 ga Oktoba, 2026.

Ya bayyana cewa an kai hare-haren ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa manyan shugabannin ’yan ta’adda da mayakansu sun taru a yankin.

Kakakin rundunar ya ce bayan kammala hare-haren, sojoji sun gudanar da bincike domin tantance illar da aka yi wa abokan gaba.

Binciken ya tabbatar da mutuwar mayaka 16, ciki har da Abu Zubiru da wasu manyan abokan hulɗarsa guda biyu da aka bayyana sunayensu da Baana Nglewa da Jindullah Sadiq.

An jikkata jagoran ISWAP

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Abu Saleem, wanda bayanan sirrin sojoji suka nuna a matsayin Wali, wato gwamnan yankin Tunbunma, ya samu munanan raunuka a lokacin harin.

Kara karanta wannan

Kungiyar Amnesty ta shiga batun kisan Sheikh Masussuka a Katsina

An ce wasu ’yan ta’adda bakwai sun samu raunuka masu tsanani tare da shi sakamakon luguden wutar sojin.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda aka kai wadanda suka jikkata domin neman magani ba, ko kuma halin da suke ciki bayan harin.

An Kashe ’yan ta’adda 37 cikin sa’o’i 72

Rundunar Operation Hadin Kai ta ce wannan sabon farmaki na daga cikin hare-haren da sojoji ke ci gaba da kai wa sansanonin ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas.

A cewar rundunar, an kashe jimillar ’yan ta’adda 37 cikin sa’o’i 72 na ci gaba da gudanar da ayyukan soji a yankin.

Sojoji sun hallaka kwamandan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda da dama

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), ta ce ta kashe ’yan ta’adda 103 a hare-haren sama bakwai da ta kai tsakanin 10 zuwa 18 ga Oktoba 2026.

Dakarun sojin sun kuma lalata cibiyoyin samar da kayayyaki da wuraren ajiyar kayan aiki da dama na yan ta'adda a wadannana hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng