Abin da Mutane ke Cewa bayan Sun Samu Tallafin N50,000 daga Gwamnatin Tarayya
- ’Yan Najeriya na ci gaba da amfani da lambobin USSD domin tantance ko an zaɓe su cikin waɗanda za su cmsamu tallafin N50,000
- Gwamnatin tarayya ta ce za ta raba tallafin ne ga zaɓaɓɓun gidaje masu rauni a matakai daban-daban
- Wadanda suka samu tallafin sun nuna farin cikinsu tare da rokon gwamnati ta ci gaba da bullo da hanyoyin tallafawa talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bincike ya nuna cewa ’yan Najeriya da dama na ziyartar bankunan intanet da aka ware ko amfani da lambobin USSD domin tantance ko sun cancanci samun tallafin N50,000.
Hakan dai na zuwa ne bayan samun labarin tallafin N50,000 da gwamnatin tarayya ta shirya bai wa ’yan ƙasa karkashin shirin NERSI.

Source: Twitter
Yadda aka fara rabon tallafin N50,000
Channels tv ta rahoto cewa a ranar 30 ga Oktoba, 2026, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin tallafin gaggawa wato National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).
Wannan mataki na shirin ya faɗaɗa ayyukan tallafin da aka gudanar a baya, inda aka tsara bayar da tallafin kuɗi na N50,000 a kowane wata ga masu karamin karfi a sassan ƙasar nan.
Ana aiwatar da shirin ne a rukuni-rukuni kamar yadda gwamnati ta yi bayani, inda ake tura kuɗin kai tsaye zuwa walat ɗin wayoyin waɗanda suka cancanta ta hannun kamfanonin hada-hadar kuɗi na zamani da aka ba lasisi.
Ra’ayoyin waɗanda suka amfana
Yayin zantawa da ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana, Mista Akila, mazaunin Nyanya Phase 4 da ke Abuja, ya tabbatar wa jaridar Tribune Nigeria cewa ya karɓi tallafin kuɗin a asusunsa na OPay.
Ya nuna godiyarsa ga gwamnatin tarayya bisa ganin ya cancanci samun tallafin, sannan ya buƙaci gwamnati ta ƙara ƙoƙari wajen rage wa ’yan ƙasa radadin matsin tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, Robert Kayi ya nuna rashin gamsuwa da tsarin zaɓen waɗanda za su amfana, inda ya yi kira ga gwamnati ta inganta hanyar raba tallafin domin mutane da dama su samu damar cin gajiyarsa.
Wani ɗan ƙasa, John Adeboye, ya bayyana cewa ya tabbatar da cancantarsa, amma har yanzu yana jiran a biya shi.
Ya ce: “Abin da nake jira yanzu shi ne a turo min kuɗin.”
Ita ma Sarah Ode ta ce da dama daga cikin ƙawayenta sun karɓi tallafin, amma ita har yanzu ba ta samu komai ba.
“Har yanzu ban karɓi komai ba, amma ina da fatan zan samu," in ji ta.
Saƙo ga wadanda ba su samu tallafin ba
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ce ana zabar wadanda za su amfana da tallafin N50,000 na wata-wata ta hanyar tsarin kwamfuta kai tsaye
Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ta ce babu bukatar cike fom, biyan kudiNko neman alaka da jami’an gwamnati ko yan aiyasa domin samun tallafin.
Asali: Legit.ng

