An Rage Mugun Iri: Yan Ta'adda Sun Gamu da Bala'in da Ya Fi Karfinsu, Sama da 100 Sun Mutu

An Rage Mugun Iri: Yan Ta'adda Sun Gamu da Bala'in da Ya Fi Karfinsu, Sama da 100 Sun Mutu

  • Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta kashe ’yan ta’adda 103 a hare-haren sama bakwai da ta kai tsakanin 10 zuwa 18 ga Oktoba 2026
  • Hare-haren sun lalata wuraren ajiyar kayayyaki da cibiyoyin samar da kayan aiki na kungiyar ISWAP a jihohin Borno da Adamawa
  • Rundunar ta ce ta kashe Jindullah, wani fitaccen mayaƙin ISWAP da ake zargin shi ne babban mai gadin Abu Saleem

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rundunar haɗin gwiwar sojoji ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK), ta ce ta kashe ’yan ta’adda 103 a hare-haren sama bakwai da ta kai tsakanin 10 zuwa 18 ga Oktoba 2026.

Dakarun sojin sun kuma lalata cibiyoyin samar da kayayyaki da wuraren ajiyar kayan aiki da dama na yan ta'adda a wadannana hare-hare.

Jirgin sojoji.
Jirgin rundunar sojojin saman Najeriya yayin da ya fito aiki Hoto: HQ Nigerian Airforce
Source: Facebook

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da wannan nasara a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook da safiyar yau Talata.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira

Rundunar ta ce hare-haren, waɗanda aka gudanar bisa bayanan sirri, sun nufi mayaƙan ƙungiyar ISWAP, shugabanninta da hanyoyin samar da kayayyakin aikinta a wasu sassan jihohin Borno da Adamawa.

Mai magana da yawun Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sojoji sun mai manyan hare-hare 7

Ya ce hare-haren sun ƙunshi haɗin gwiwar jiragen sama na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, rundunar jiragen sama marasa matuƙa ta sojin ƙasa (NARPAS) da kuma jiragen rundunar sojin sama.

Ya ce an gudanar da ayyukan ne domin tarwatsa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda, katse hanyoyin samar musu da kayayyaki da kuma hana su samun ’yancin gudanar da ayyukansu.

A cewar Goni, hare-haren bakwai sun shafi wuraren ’yan ta’adda da ke kusa da Gudumbali a ƙaramar hukumar Guzamala a ranar 10 ga Oktoba; da Badu a ƙaramar hukumar Monguno a ranar 11 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun hallaka sojojin Najeriya a wani yanayi mara dadi a Borno

Sai kuma yankin Mairari a Guzamala da wani yanki da ke gabashin Badu a ranar 13 ga Oktoba; da kuma Duste Uku a ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa a ranar 16 ga Oktoba.

An kashe manyan mayaƙan ISWAP

Goni ya ce an kai harin na ranar 18 ga Oktoba ne bayan tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan sa ido da bincike kan gidan zama na daban na Abu Saleem.

Ya ce bayanan sirri da aka tattara daga mutane daga baya sun tabbatar da kashe Jindullah, wanda aka bayyana a matsayin fitaccen kwamandan ISWAP da ake zargin ya kasance babban mai tsaron lafiyar Abu Saleem.

Bayanan sun kuma tabbatar da mutuwar Abul Kissa, wanda aka bayyana a matsayin mamba a majalisar Shura ta ƙungiyar, tare da wasu fitattun mayaƙa a wurin da aka kai harin.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A cewar kakakin rundunar, harin ya lalata ginin da muhimman kayayyakin aikin ƙungiyar, ciki har da injunan kwale-kwale guda tara da babura da dama da aka ajiye a wurin.

Ya ce harin ya kuma tarwatsa tsarin da ’yan ta’addan ke amfani da shi wajen ɓuya a yankin dazuzzuka, lamarin da ya ƙara raunana damar amfani da wurin a matsayin mafaka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan daba ɗauke da makamai sun kewaye jigon APC, sun kashe shi nan take

Ya danganta nasarorin da aka samu da ayyukan da aka gudanar bisa bayanan sirri da haɗin gwiwar rundunar jiragen sama ta sojin ƙasa, NARPAS, rundunar sojin sama da dakarun ƙasa.

Sojoji sun kashe jagora a ISWAP

Kun ji cewa sojojin Najeriya, DSS da jami'an Amotekun sun hallaka wani babban shugaban ISWAP, Abdussamad Ohida, a wani samame da aka kai maboyar 'yan ta'adda a Ondo.

Majiyoyin tsaro sun ce Ohida ya taba zama mataimakin shugaban ISWAP a wasu yankunan Najeriya bayan kama Abu Ikrimah, wanda aka fi sani da Abu Uwais.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262