Kotu Ta Yi Hukunci kan Wani Matashi da Ya Yi Barazanar Sakin Hotunan Tsiraicin Gwamna Abba

Kotu Ta Yi Hukunci kan Wani Matashi da Ya Yi Barazanar Sakin Hotunan Tsiraicin Gwamna Abba

  • Kotu ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan Sanusi Dankaka, wanda ake zargi da barazanar yaɗa bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamna Abba Yusuf na Kano
  • Mai gabatar da ƙara ya nemi janye ƙarar, kuma lauyan wanda ake zargi bai yi adawa da buƙatar ba
  • Hukumar DSS ta zargi Dankaka da aikata laifukan yanar gizo ta hanyar shafinsa na Facebook

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a ƙarar da aka shigar kan wani matashi, Sanusi Dankaka, wanda ake zargi da barazanar yaɗa bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kotun tarayya ta kori karar gaba daya bayan bangaren masu kara sun sanar da janyewa, kuma lauyan wanda ake tuhuma bai yi musu ba.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ɗan agajin Izala kan zargin barazana ga Kiristoci a bidiyo

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a taron magoya baya a fadar gwamnatinsa Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hukuncin da kotu ta yanke

Jaridar Vanguard ta rahoto cwwa Mai shari’a Salim Ibrahim na babbar kotun tarayya ne ya yanke hukuncin watsi da ƙarar a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba, 2026.

Lauyan wanda ake zargi, Kauna Penzin, bai yi adawa da buƙatar janye ƙarar ba. Daga nan ne alƙalin ya yanke hukuncin yin watsi da ƙarar a taƙaice.

Duk da cewa mai shari’a Ibrahim ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga Disamba, 2026 bayan wanda ake zargi ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su, an sake saka karar a shari’o’in da za a saurara a ranar Talata.

Leadership ta ruwaito cewa an gurfanar da Dankaka ne bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi laifuffukan yanar gizo.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a cikin takardar tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CR/699/2026, da t shigar a ranar 22 ga Oktoba, ta zargi wanda ake tuhuma da aikata laifin a watan Oktoba na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Wadanda suka kashe Sheikh Masussuka sun fito sun bayyana kan su

Abin da DSS ke zargin sa

A tuhuma ta farko, an zargi Dankaka da wasu mutanen da har yanzu ba a kama ba, waɗanda ke zaune a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato, da ƙoƙarin yaɗa wani saƙo mai cutarwa ta shafinsa na Facebook mai suna “Sanusi Dankaka Yahaya”.

Ana zargin ya bayyana cewa yana da bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamna Abba, tare da barazanar fitar da su ga jama’a.

Dakarun DSS.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS a bakin aiki Hoto: @OfficialDSS
Source: Twitter

DSS ta ce hakan ya saɓa wa Sashe na 27(1)(6) na Dokar Laifuffukan Yanar Gizo ta 2015, kamar yadda aka yi wa dokar gyara, kuma ana hukunta laifin a ƙarƙashin Sashe na 24(1) na dokar.

Yadda DSS ta gurfanar da matashin

Kun ji cewa Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Sanusi Dankaka a Kuje bayan an gurfanar da shi kan tuhume-tuhume biyu na laifuffukan yanar gizo.

DSS ta zargi Dankaka da ikirarin cewa yana da bidiyo da hotunan tsiraicin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da barazanar wallafa su a Facebook.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa dangane da gwamnan na jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262