Mazan Fama: Amurka Ta Yaba Wa Sojojin Najeriya bayan Gudanar da Wani Gagarumin Aiki
- Amurka ta yaba wa sojojin Najeriya kan ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su yayin samamen da suka gudanar daga 6 zuwa 12 ga Nuwamba
- Hedikwatar Tsaro ta ce sojoji sun kashe ’yan ta’adda takwas, sun kama waɗanda ake zargi da taimaka musu 10, yayin da mayaƙa 12 suka miƙa wuya
- Daga cikin waɗanda aka ceto akwai matafiya 119 da aka sace a hanyar Dutsen Kura zuwa Bulazarma da Kamuya a jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Amurka ta yaba wa rundunar sojin Najeriya kan ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su, tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda yayin hare-haren soji da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar cikin wannan watan.
Ofishin Harkokin Afirka na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

Source: Twitter
Ofishin Harkokin Afirkan na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurkan ya wallafa sanarwar ne a shafinsa na X ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026.
A cikin sanarwar ya yaba wa sojojin kan ƙwato makamai da kuma gano tare da kawar da bama-bamai da aka binne a wurare daban-daban.
Amurka ta yaba wa nasarorin sojojin Najeriya
A cikin sanarwar, ofishin ya ce:
“Amurka na yaba wa ayyukan sojojin Najeriya da aka gudanar a wannan watan, waɗanda suka kai ga ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su, lalata sansanonin ’yan ta’adda, ƙwato makamai da kuma kawar da bama-bamai.”
Ofishin ya ƙara da cewa Amurka na goyon bayan ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na hana sace mutane da kuma tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu a aikata irin waɗannan laifuka sun fuskanci hukunci.
Sanarwar ta ce:
"Muna goyon bayan duk wani ƙoƙari da gwamnatin Najeriya ke yi na hana sace mutane da kuma tabbatar da cewa waɗanda ke da hannu wajen aikata wannan ta’asa sun ɗauki cikakken alhaki.”
Sojoji sun ceto matafiya 119 a Borno
Yabon da Amurka ta yi ya biyo bayan hare-haren sojoji da aka gudanar tsakanin 6 zuwa 12 ga Nuwamban 2026.
A cewar Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, sojoji sun ceto mutane 125, sun kashe ’yan ta’adda takwas tare da kama mutum 10 da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda da kuma samar musu da kayan aiki.
Hare-haren sun kuma kai ga mayaƙan ’yan ta’adda 12 da iyalansu sun miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Babban aikin ceton ya shafi matafiya 119 da aka yi garkuwa da su ranar 6 ga Nuwamba a kan hanyar Dutsen Kura-Bulazarma-Kamuya, da ke Buratai, ƙaramar hukumar Biu a jihar Borno.
Bayan samun labarin sace mutanen, sojoji sun bi sawun maharan, lamarin da ya tilasta musu barin waɗanda suka yi garkuwa da su. Mutanen da aka ceto sun ƙunshi maza 69, mata 35 da yara 15.
An kuma ceto wasu mutane a Zamfara
Baya ga mutanen da aka ceto a Borno, sojoji sun kuma kuɓutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan daban-daban a jihar Zamfara.
A sauran wuraren da aka gudanar da hare-haren, sojoji sun ƙwato makamai da alburusai, sun lalata sansanonin ’yan ta’adda tare da gano da kuma kawar da bama-bamai da aka ƙera da kayan fashewa.
Yabon da Amurka ta yi wa sojojin Najeriya na zuwa ne a lokacin da ƙasashen biyu ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannin tsaro, domin tunkarar matsalolin da ke addabar Najeriya.

Source: Twitter
Tinubu ya fitar da sabon tsarin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wani sabon shirin tsaro na shekara biyar da aka tsara domin kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Majalisar ta ce shirin zai karfafa tsarin tsaron kasar, inganta ayyukan sojoji da kuma tabbatar da hadin gwiwa wajen tinkarar sababbin barazanar tsaro.
Asali: Legit.ng

