Jihohi 24 da Aka Amince a Kafa ‘Yan Sandan Jiha da Sauran 12 da Suke Jan Kafa

Jihohi 24 da Aka Amince a Kafa ‘Yan Sandan Jiha da Sauran 12 da Suke Jan Kafa

  • Majalisun dokokin jihohi sama da 20 sun amince da kudirin kafa ’yan sanda a jihohi a kasar nan
  • Jihohi 12, ciki har da Kano, Katsina da Bauchi da kuma wasu a Kudu ba su amince da kudirin ba tukuna
  • Kudirin na neman sauya kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan tarayya da na musamman a jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Majalisun dokokin jihohi 24 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya da nufin inganta tsaro.

‘Yan majalisa sun ba jihohi damar kafa rundunonin ’yan sanda nasu ban da dakarun da ke karkashin gwamnatin tarayya.

'Yan sanda
Jami'an 'Yan sanda a bakin aiki a Legas Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yunkurin samar da 'yan sanda a jihohi

Jaridar Vanguard ta tattaro yadda maganar ta yi nisa, ta kawo jerin jihohin da suka amince da kudirin kafa ’yan sandan jihohi.

Akwai sharadin samun amincewar akalla kashi biyu bisa uku na jihohi 36 da ake buƙata kafin a iya gyara kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Jama’a sun ji haushin Sanusi II da sarki ya kawo shawarar gyara tattalin arziki

Ondo ce jihar farko da 'yan majalisar ta suka yi na'am da wannan kudiri tun a watan Satumban 2026.

Jihohi 24 da suka amince a kafa ‘yan sandan jiha

  1. Adamawa
  2. Delta
  3. Edo
  4. Kwara
  5. Nasarawa
  6. Ogun
  7. Osun
  8. Oyo
  9. Filato
  10. Rivers
  11. Taraba
  12. Zamfara
  13. Enugu
  14. Anambra
  15. Imo
  16. Ekiti
  17. Kebbi
  18. Akwa Ibom
  19. Bayelsa
  20. Benue
  21. Cross River
  22. Abia
  23. Yobe
  24. Kaduna

Jihohin da ba su amince da kudirin ba

Jihohi 12 ne har yanzu ake jiran matsayarsu kan kudirin. Sun hada da jihohi uku daga Kudu da tara daga Arewa.

Rahoton da aka samu daga tashar TVC ya nuna jihar Legas tana cikin wannan sahu zuwa yanzu.

Shugaban kwamitin yada labarai da dabaru na majalisar dokokin jihar Legas, Stephen Ogundipe, ya ce suna hutu a yanzu.

Yake cewa ana sa ran ’yan majalisar za su koma aiki a mako mai zuwa, inda za su tattauna kudirin, su yi abin da ya dace.

Jihohin su ne:

  1. Legas
  2. Ondo
  3. Ebonyi
  4. Kogi
  5. Neja
  6. Borno
  7. Gombe
  8. Bauchi
  9. Jigawa
  10. Katsina
  11. Kano
  12. Sokoto

Kara karanta wannan

Tinubu: Nasir El Rufai ya daura bidiyon abin da Sarkin Katsina ya fada wa Abdulaziz Yari

Halin da kudirin yake ciki a sauran jihohi

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta shiga cikin jihohin da suka amince da kudirin a ranar Alhamis dinnan da ta wuce.

’Yan majalisar sun amince da gyaran wasu sassa 15 na kundin tsarin mulkin 1999 domin a kafa ’yan sanda na jihohi.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar ya ce tsarin zai inganta tsaro kuma ya kare rayuka da dukiyoyin jihar.

Baya ga haka, Hon. Henry Marah ya ce kudirin zai samar da ayyukan yi ga matasa a Kaduna.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin Abia, Austin Nmeregini, ya tabbatar da cewa majalisar ta amince da kudirin.

A jihar Gombe, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Aliyu Baba Manu, ya ce ba a gabatar masu da kudirin ba ma.

Shugaban majalisar dokokin jihar Ebonyi, Moses Ije Odunwa, ya ce ’yan majalisarsa sun fara tattaunawa game da batun.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Ondo, Olatunji Oshati, ya ce an raba masu takardun kudirin su yi nazari a kan shi.

Kara karanta wannan

Bayan kama su da laifi, za a rataye jami'an tsaro 3 har lahira a Arewacin Najeriya

Majalisar jihar Kogi ba ta fara zama domin tattauna kudirin ba. Ana sa ran idan sun dawo daga kasar Rwanda su fara aikin shi.

Jami'an 'Yan sanda
Wani 'dan sanda yana gadin gidan gwamna a Ikeja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ayyukan Gwamnatin tarayya a jihohin Arewa

Dazu aka ji labari Bayo Onanuga ya fitar da jerin tituna da aikin jirgin kasa da Bola Tinubu yake yi wa a jihohin Arewa.

Hadimin shugaban kasar ya rufe bakin ‘yan adawa da suke cewa ba su ci moriyar komai ba a gwamnatin mai-ci.

Ban da karasa titin Abuja-Kaduna-Kano, akwai hanya da za a yi tun daga Sokoto har Legas kuma an soma yin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng