Obi Ya Bukaci Bola Tinubu Ya Koma Gida Ya Huta, Ya bar Maganar Takarar 2027

Obi Ya Bukaci Bola Tinubu Ya Koma Gida Ya Huta, Ya bar Maganar Takarar 2027

  • Peter Obi ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da kuzarin da ake buƙata wajen jagorantar Najeriya, inda ya buƙaci ya bar mulki bayan zaɓen 2027
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ya zargi gwamnatin APC da gaza magance talauci, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da matsalar tsaro
  • Obi ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan samar da mafita ga matsalolin ƙasar, maimakon ɗora wa wasu laifi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ba shi da kuzari da jajircewar da ake buƙata wajen jagorantar Najeriya.

Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya buƙaci Tinubu ya koma gida, yana mai cewa Najeriya na buƙatar shugaban da zai kasance a shirye domin tunkarar matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya sake neman alfarmar yan Najeriya yayin kamfen a Kaduna

Dan takarar NDC, Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ƙasa na jam’iyyar NDC.

Obi ya ce Tinubu ya koma gida

A wajen taron, Obi ya ce Najeriya na buƙatar shugaban da zai kasance a ko da yaushe a shirye wajen gudanar da ayyukan mulki, musamman ganin yadda ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da tsaro.

Ya ce:

“Fiye da komai, Shugaba Tinubu ba shi da kuzari da jajircewar da ake buƙata domin jagorantar Najeriya a yau, kuma dole ne ya koma gida.
“Muna buƙatar ya koma gida. Ba za a iya mulkin Najeriya da irin kuzarin da yake da shi a yau ba. Najeriya na buƙatar shugaban da zai kasance a shirye kuma ya kasance tare da jama’a.”

Obi ya kuma zargi gwamnatin jam’iyyar APC da ƙara ta’azzara talauci, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Wike ya faɗi abin da zai hana Obi zama shugaban ƙasa, ya tuna mummunan halinsa 1

Ayyukan da Obi zai yi

Obi ya ce gwamnatinsa ba za ta riƙa ɗaura wa wasu laifi ba, sai dai ta mayar da hankali kan nemo hanyoyin magance matsalolin ƙasar.

Punch ta rahoto ya ce:

“Manufar mulki ita ce magance matsaloli, ba ɗaura wa mutane laifi ba. Ba zan ɗaura wa kowa laifi ba. Za mu samar da sabuwar Najeriya.”
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Obi ya yi alƙawarin yaƙi da cin hanci

Ɗan takarar na NDC ya bayyana cin hanci da rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban Najeriya.

Ya yi alƙawarin ƙaddamar da yaƙi mai ƙarfi da wannan matsala idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Obi ya ce:

“Muna buƙatar juyin-juya-hali da zai sauya wannan ƙasa, kuma mun ƙuduri aniyar yin hakan. Gwamnatin APC ƙarƙashin Shugaba Tinubu ta gaza wajen yi wa Najeriya aiki.”

An kama mai goyon bayan Atiku

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da wani magoyin bayan Atiku Abubakar mai suna Mubarak Abdullahi bisa zargin yaɗa wata takarda ta ƙarya da aka danganta da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Buhari ta wulakanta Tinubu duk da sadaukarwar da ya yi mata

An kama Mubarak ne a ranar 28 ga Satumba bayan zargin ya wallafa takardar a shafinsa na Facebook tare da rubuta cewa 'Atiku na zuwa.'

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, wanda ake zargin ya amince wa masu bincike cewa ya wallafa takardar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng