Yan Sandan Jihohi: Gwamna Ya Bukaci a Ɗauki Matasa Sama da 500,000 Aiki a Najeriya

Yan Sandan Jihohi: Gwamna Ya Bukaci a Ɗauki Matasa Sama da 500,000 Aiki a Najeriya

  • Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya ce Najeriya na buƙatar ƙarin jami’an tsaro 554,353 domin samar da isassun ma’aikata a tsarin ’yan sandan jihohi
  • Ya buƙaci kafa Asusun Fara Aiki na ’Yan Sandan Jihohi saboda kada bambancin ƙarfin kuɗin jihohi ya kawo cikas ga tsarin
  • Abiodun ya ce muhawarar yanzu ba ita ce ko Najeriya na buƙatar ’yan sandan jihohi ba, illa yadda za a kafa tsarin cikin gaggawa kuma mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya ce Najeriya na buƙatar ƙarin jami’an tsaro 554,353 domin samun isassun ma’aikata a tsarin ’yan sandan jihohi da ake shirin kafawa.

Gwamna Abiodun, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudancin Najeriya ya bukaci a dauki adadin wadannan jami'ai domin cike gibin da ake da shi a bangren dakarun tsaro.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Gwamnan Osun.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun yana jagorantar taro a fadar gwamnati da ke Abeukuta Hoto: Prince Dapo Abiodun
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Abiodun ya kuma yi kira da a kafa Asusun Fara Aiki na Musamman na ’Yan Sandan Jihohi domin tabbatar da cewa bambancin ƙarfin kuɗin jihohi bai kawo cikas ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin gabatar da babban jawabi a taron tunawa da cikar marigayi tsohon Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, da aka gudanar a Cibiyar Taron Ƙasa ta Jami’ar Ibadan.

Adadin yan sandan da ake bukata

Abiodun, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kan ’Yan Sandan Jihohi ya ce batun ’yan sandan jihohi ya wuce matakin kira da a kafa rundunar yan sandan.

A cewarsa, bayanan Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, bisa ma’aunin Majalisar Ɗinkin Duniya na jami’in ɗan sanda ɗaya ga mutane 414, sun nuna cewa Najeriya na buƙatar ƙarin jami’ai 554,353.

Gwamnan ya ce domin cike wannan gibi, akwai bukatar ɗaukar kusan yan sanda 184,784 a kowace shekara na tsawon shekaru uku.

Kara karanta wannan

Hukumar fanshon ƴan sanda za ta zuba hannun jari a matatar Dangote

“Yanzu muhawarar ba ita ce ko Najeriya na buƙatar ’yan sandan jihohi ba, illa yadda za mu kafa su cikin gaggawa kuma ta hanyar da za ta ɗore,” in ji Abiodun.

Gwamna ya nemi canza tsarin tsaro

Ya ce ba zai yiwu Najeriya ta iya ci gaba da tsarin tsaro da ya dora nauyin aikin ’yan sanda ƙarƙashin gwamnatin tarayya ba, yana mai jaddada buƙatar kusantar da aikin ’yan sanda ga jama’a.

“Tsaro yana da alaƙa kai tsaye da al’umma. Ba za ka iya kula da al’ummar da ba ka jin yarenta ko kuma ba ka san yanayinta da wuraren da take ba.

"’Yan sandan jihohi ba barazana ba ne ga haɗin kan ƙasa; su ne ginshiƙin zaman lafiya da bunƙasa,” in ji shi.
Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Sai dai Abiodun ya yi gargadin cewa dole ne a magance matsalolin kuɗin jihohi kafin tsarin ’yan sandan da ake shirin kafawa ya zama mai tasiri.

“Rashin tsaro a jihohin da ke da ƙarancin kuɗin shiga yana yaɗuwa zuwa ƙasa baki ɗaya. Rashin isasshen kuɗaɗen ’yan sanda a jiha ɗaya ya zama matsalar kowa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yaba wa Sarki Aminu Ado kan muhimmin abin da ya yi

Saboda haka, gwamnan ya nemi a kafa Asusun Fara Aiki na ’Yan Sandan Jihohi ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki, inda za a samar da tallafin da ya dace ga kowa.

Majalisa ta amince a kafa yan sandan jihohi

Kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan.jihohi domin magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar ta amince da gyaran kundin tsarin mulki don kafa yan sandan jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262