An Shiga Tashin Hankali da Sojojin Najeriya Suka Tare Wasu Matasa, Suka Harbe Su har Lahira
- An zargi sojojin da ke aiki da wani kamfanin haƙar ma’adinai da kashe matasa biyu a Ihetutu, jihar Ebonyi
- Mahaifin ɗaya daga cikin matasan ya yi zargin cewa sojojin sun harbe su ne bayan sun ƙi ba su kuɗin da suka nema daga hannunsu
- Mutanen yankinnsun yi Allah wadai da lamarin, tare da buƙatar gwamnatin jihar Ebonyi ta gudanar da cikakken bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ebonyi, Nigeria - An shiga alhini da tashin hankali a Ihetutu, al’ummar Ishiagu da ke ƙaramar hukumar Ivo a jihar Ebonyi, ranar Lahadi, bayan zargin wasu sojojin Najeirya d kashe matasa biyu.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin da da ake zargi da wannan kisa suna aiki ne da wani kamfanin haƙar ma’adinai.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa an bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Chibuike Elema, mai shekaru 18, da Obinna Joshua, mai shekaru 19.
Mazauna yankin sun nemi adalci
Rahotanni sun nuna cewa an harbe matasan har lahira ne da tsakar ranar Lahadi da ta gabata a wani wurin haƙar ma’adinai da kamfanin Palladium Mining Company ke gudanarwa, bayan sun ƙi ba wa sojojin da aka girke domin tsaro, kuɗi.
Lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin al’ummar, inda mazauna yankin, musamman mata da shugabannin al’umma, suka buƙaci gudanar da cikakken bincike.
Sun kuma bukaci hukumomi su kawo ƙarshen abin da suka bayyana a matsayin tsauraran matakan da kamfanin haƙar ma’adinan da jami’an tsaro ke ɗauka kan ’ya’yansu.
Yadda aka kashe matasa a Ebonyi
Mista Donatus Okoro, mahaifin Chibuike Elema, ya ce an kira ɗansa daga gida a safiyar Lahadi domin ya haɗu da sauran ma’aikata a wurin haƙar ma’adinan.
Ya ce shaidun gani da ido sun gaya masa cewa matasan na dawowa daga aiki ne lokacin da sojojin da ke aiki da kamfanin Palladium Mining Company suka nemi su ba su kuɗi.
Ya yi zargin cewa sojojin sun buɗe musu wuta ne bayan sun bayyana cewa ba su da kuɗin da za su ba su.

Source: Original
Okoro ya ce:
“An kira ɗana daga gida da safe domin ya zo ya haɗu da sauran ma’aikata su yi aikin ranar Lahadi.
"A lokacin da suke dawo, a cewar mutanen da suka ga abin da ya faru, sojojin da ke aiki da wani kamfanin haƙar ma’adinai mai suna Palladium sun nemi su ba su kuɗi.
"Amma suka gaya wa sojojin cewa ba su da komai a hannunsu. Sai sojojin suka ɗaga bindigoginsu suka harbe su a kai.”
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Ebonyi da ta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa an hukunta waɗanda aka samu da hannu a kisan.
An sace mahaifin tsohon mataimakin gwamna
Kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Francis Igwe, mahaifin tsohon mataimakin gwamnan Ebonyi , Dr. Kelechi Igwe.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa coci, inda ‘yan bindiga kan babur suka tare motarsa.
Asali: Legit.ng

