'Yan Ta'adda kan Babura Sama da 100 Sun Gamu da Abin da Ya Fi Karfinsu a Daji

'Yan Ta'adda kan Babura Sama da 100 Sun Gamu da Abin da Ya Fi Karfinsu a Daji

  • Sojojin Operation Fansan Yamma sun dakile harin da mayakan Lakurawa suka kai sansanin sojoji na FOB Maiyama a jihar Kebbi
  • Maharan sun zo da babura sama da 100, dauke da manyan bindigogi da makaman harba rokoki
  • Sojoji sun kwato babura 17 da aka bari, tare da bindigogi, harsasai da na’urorin sadarwa da ake zargin maharan sun yi amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun dakile wani hari da mayakan kungiyar ’yan ta’addar Lakurawa suka kai sansanin sojoji na FOB Maiyama, a jihar Kebbi.

'Yan ta'addan na Lakurawa sun kai harin ne da sanyin safiyar ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2026.

Sojoji sun dakile harin 'yan Lakurawa
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

’Yan ta’adda sun zo kan babura 100

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da 'yan ta'adda suka hallaka sojoji da dan kasar waje a Kebbi

A cewar majiyoyin tsaro, maharan da yawansu ya yi yawa sun zo ne da babura sama da 100, da nufin mamaye sansanin sojojin.

Rahoton ya ce maharan na ɗauke da manyan bindigogin da kuma makaman harba rokoki, waɗanda suka yi amfani da su wajen kai farmaki kan sojojin.

Sai dai dakarun sun kare sansanin, suka mayar da martani da ƙarfin makamai, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya cikin rudani zuwa wuraren da ke kewaye da sansanin.

An kashe wasu maharan, wasu sun tsere da raunuka

Rahoton ya bayyana cewa an kashe wasu daga cikin maharan yayin musayar wuta, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Bayan fatattakar maharan, sojojin sun gudanar da aikin bincike da bin sawunsu, inda suka gano babura 17 da suka bari yayin tserewa.

Sojoji sun kwato makamai da na’urorin sadarwa

Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun kuma kwato bindigar PKT, bindigar AK-47, harsasai da dama da kuma na’urorin sadarwa na Baofeng da ake zargin maharan sun yi amfani da su yayin harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan kai kazamin hari a Kebbi

Yankin na ci gaba da kasancewa ƙarƙashin ikon sojoji, yayin da suke gudanar da sintiri da ayyukan tsaro domin gano sauran ’yan kungiyar da suka tsere.

Duk da nasarar dakile harin, ana ci gaba da sintiri da bin diddigin maharan domin tabbatar da tsaro a yankin.

Harin da 'yan ta'addan suka kai ya kara nuna girman barazanar matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a jihar.

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan Lakurawa
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

'Yan ta'adda sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan ta'adda da ake zargin ’yan kungiyar Lakurawa ne sun kashe sojoji biyu da wani ɗan China a wani hari da suka kai wa ma’aikatan gina hanya a jihar Kebbi.

Harin ya faru ne ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026 a ƙaramar hukumar Maiyama, lokacin da maharan suka kai wa ma’aikatan hari ba zato ba tsammani.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ya bayyana cewa maharan sun kashe sojojin biyu da ɗan China, yayin da wasu mutane da dama suka samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng