'Yan Ta'adda Sun Hallaka Sojojin Najeriya a Wani Yanayi Mara Dadi a Borno

'Yan Ta'adda Sun Hallaka Sojojin Najeriya a Wani Yanayi Mara Dadi a Borno

  • Akalla sojoji takwas sun mutu sakamakon fashewar nakiyar da motar sintirinsu ta taka a kauyen Kinuba, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru
  • Wani mamban rundunar sa-kai ya ce an tayar da nakiyar daga nesa, yayin da fashewar ta raunata wani mutum da ke aikin share dazuzzuka
  • Harin ya faru a ranar da babban hafsan sojin kasa, Waidi Shaibu, ya ziyarci Maiduguri bayan wani hari da ya kashe sojoji 15 da mambobin sa-kai biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Akalla sojoji takwas sun mutu bayan motar sintirinsu ta taka nakiyar da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP suka binne a jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoban 2026 a kauyen Kinuba, mai tazarar kilomita 25 daga Gamboru, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

Kara karanta wannan

Tsugune ba ta kare ba, Amurka ta sake barazanar janye taimakonta ga Najeriya

'Yan ISWAP sun kashe sojoji a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Yadda harin ya faru

Rahotan jaridar TheCable ya ce sojojin na duba aikin mambobin wata rundunar sa-kai da ke taimaka wa sojoji wajen yaki da ’yan ta’adda.

Mambobin rundunar sa-kan na share dazuzzuka domin kakkabe 'yan ta'adda a gefen wata babbar hanya a wajen Gamboru.

A yayin aikin, motar sojojin ta taka wani abu mai fashewa. Wani jami’in soja da ke yankin ya ce dukkan sojoji takwas da ke cikin motar sun mutu sakamakon fashewar.

Ibrahim Liman, wani mamban rundunar sa-kai da ke taimaka wa sojojin, shi ma ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP da adadin wadanda suka mutu.

Liman ya ce an binne nakiyar ne a wata hanya mai kura, sannan aka tayar da ita daga nesa ta hanyar amfani da igiyar tayar da nakiyar.

Ya kara da cewa fashewar ta raunata wani mamban rundunar sa-kai da ke sa ido kan aikin share dazuzzukan.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Harin ya zo bayan kisan sojoji 15

Harin ya faru ne a ranar da babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Waidi Shaibu, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ziyarar ta biyo bayan wani hari da aka kai sansanin soji kwanaki kadan da suka gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji 15 da kuma mambobin rundunar sa-kai biyar.

ISWAP, wadda ke da alaka da kungiyar Islamic State, tana gudanar da ayyukanta a yankin.

Mayakan ’yan ta’addan kan yi amfani da ciyayi da dazuzzukan da ke gefen hanyoyi wajen boyewa da kai wa sojoji da matafiya kwanton bauna.

Sauran hare-haren da aka kai

A ranar 8 ga Oktoba, rundunar sojin Najeriya ta ce wasu sojoji sun mutu bayan ’yan ta’adda sun kai wani hari da ta bayyana a matsayin “farmaki mai tsari daga wurare daban-daban” a Kukawa, jihar Borno.

Haka kuma, a watan Agusta, wani soja ya mutu yayin wani samame da aka gudanar domin dakile hare-haren ’yan ta’adda da suka nufi barikin soji da wasu al’ummomi biyu a karamar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Bayan murabus a gwamnatin Tinubu, INEC ta saka sunan tsohon minista ya yi takara

An kashe sojoji a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun samu nasara kan 'yan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar wani babban hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansaninsu a Borno

​Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun yi asarar rayuka masu yawa, inda aka kashe fiye da 25 daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng