Rashin Tsaro: Mutanen Gari Sun Huce Fushinsu kan Mataimakin Gwamnan Zamfara
- Mutanen Gwashi sun yi wa Mataimakin Gwamnan Zamfara, Mani Mummuni, ihu lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya bayan harin da ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula
- Wasu mutane sun ce hare-haren ’yan bindiga sun hana su fita sayen kayan masarufi har na tsawon kwanaki shida zuwa bakwai
- Yayin da wasu shaidu suka ce matasa sun kai hari kan ayarin motocin mataimakin gwamnan, wani daga cikin tawagarsa ya musanta hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wasu matasa da fusatattun mutanen kauyen Gwashi, da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, sun yi wa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ihu tare da kai hari kan ayarin motocinsa.
Lamarin ya faru ne lokacin da mataimakin gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya kauyen ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoban 2026 bayan harin makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula tara.

Source: Original
Mutane sun nuna fushinsu kan matsalar tsaro
Wani mazaunin yankin da ya yi magana da jaridar Daily Trust bisa sharadin ɓoye sunansa, ya ce mutane sun fusata da mataimakin gwamnan da gwamnatin jihar saboda matsalolin tsaro da suke fuskanta.
Ya bayyana cewa Gwashi na daga cikin manyan mazabu a ƙaramar hukumar, amma a cewarsa, shugabannin jihar ba su nuna isasshiyar damuwa kan matsalolin yankin ba.
“Lokaci na ƙarshe da suka ziyarce mu ya wuce shekaru uku da suka gabata. Sun zo ne a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023. Tun daga lokacin, ba mataimakin gwamnan ba, ko wata tawagar gwamnatin jihar da ta sake zuwa domin nuna damuwa kan ƙalubalen tsaronmu da ke ƙaruwa."
“A yau mun nuna wa duniya halin da muke ciki. Mun sha bayyana koke-kokenmu, amma ba a ɗauki mataki kan rashin tsaro da rashin ayyukan raya ƙasa ba.” In ji shi
Mutumin ya ƙara da cewa bayan hare-haren ’yan bindiga, al’ummar sun shafe kwanaki shida a jere ba tare da fita sayen kayan masarufi ba, Leadership ta kawo labarin.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun tare 'yan kasuwar da ke samun rakiyar sojoji a Zamfara, an rasa rayuka
“Mun shafe kwanaki shida zuwa bakwai ba tare da fita daga kauyenmu ba. Jami’an tsaro sun daina yi wa mutane rakiya, kuma babu wanda zai iya yin kasadar fita ya rasa ransa."
“Idan muka ƙara shafe wasu kwanaki a haka, ku yarda da ni, har gishiri zai iya ƙarewa a yankin.” In ji shi.
An koka kan rashin hanyoyi da muhimman abubuwa
Mazaunin ya kuma koka kan rashin muhimman abubuwan more rayuwa a Gwashi, yana mai cewa al’ummar ba su da hanyar mota mai kyau, ingantaccen asibiti ko ruwan sha mai tsafta.
“Ba mu da hanyar shiga al’ummarmu, ba mu da asibiti mai kyau, kuma ba mu da ruwan sha mai tsafta. Gine-ginen makarantunmu sun lalace.” In ji shi.
Wani mazaunin yankin, wanda shi ma ya yi magana bisa sharadin ɓoye sunansa, ya ce makarantar sakandaren kauyen ta lalace matuƙa, har dabbobi suke amfani da harabar wajen fakewa.
Ya ce mata, yara, matasa da tsofaffi sun fito domin bayyana koke-kokensu ga mataimakin gwamnan da kuma nuna rashin gamsuwarsu da gwamnatin jihar.
“Mun fito da yawa, mata, yara, matasa da tsofaffi suna yi wa mataimakin gwamnan ihu tare da rera ‘Bamayi, Bamayi’, ma’ana ba za mu yi ba."

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
“Mun san ya zo ne domin neman ƙuri’u, kuma ba za mu zaɓe su ba.” In ji shi.
An samu saɓani kan ko an kai hari kan ayarin motocin
Mutumin ya ƙara da cewa fusatattun matasa sun kai hari kan ayarin motocin mataimakin gwamnan, inda ya yi zargin cewa an lalata wata mota.
“Mataimakin gwamnan ma da kyar ya tsira, kuma an lalata wata mota.” In ji shi.
Sai dai wani mamba a tawagar mataimakin gwamnan, wanda shi ma ya nemi a ɓoye sunansa, ya musanta cewa an kai hari kan ayarin motocin.
Ya ce masu zanga-zangar suna kusa da kasuwa ne, yayin da taron mataimakin gwamnan ya gudana kusa da asibitin kauyen.
"Abin da suke faɗa ba gaskiya ba ne. Mun kasance a wani wuri dabam kwata-kwata. Motar da suke cewa an lalata, motar jami’an tsaro ce da ta samu matsalar inji. Daga baya aka ja ta aka tafi da ita.” In ji shi.
An yi zargi kan jami’an tsaro
Wata majiya ta kuma bayyana cewa mataimakin gwamnan ya samu rakiyar jami’an tsaro da dama, waɗanda suka hana jama’a kusantar wurin da ya yi wa wasu bayani kan matsalar rashin tsaro.
“Yawan jami’an tsaron da aka tura ya hana mutane kusantar wurin domin bayyana koke-kokensu. Duk da haka, mun yi wa mataimakin gwamnan ihu tare da jifan ayarin motocinsa da duwatsu."
“Mataimakin gwamnan ma da kyar ya tsira saboda matasan sun fusata kan rashin kulawar gwamnati da rashin ɗaukar matakin da ya dace.” In ji shi.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hare-hare
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu manoma biyar sun rasa rayukansu, an sace mutane 18, yayin da ake zargin ’yan bindiga sun kona gidaje da shaguna a wasu al’ummomin jihar Niger.
Hare-haren an kai su ne a al’ummomin Fanga da ke ƙaramar hukumar Mashegu, da Kigbere da Kokani a ƙaramar hukumar Borgu.
Asali: Legit.ng

