Yan Bindiga da Ke Guduwa zuwa Zamfara Sun Tsaya a Hanya, Sun Yi Barna a Niger

Yan Bindiga da Ke Guduwa zuwa Zamfara Sun Tsaya a Hanya, Sun Yi Barna a Niger

  • ’Yan bindiga sun kashe manoma biyar, sun sace mutane 18, tare da kona gidaje da shaguna a wasu al’ummomin jihar Niger
  • Mazauna Fanga sun ce ’yan bindigar sun ci gaba da kai hare-hare duk da karɓar haraji sau biyar, lamarin da ya tilasta masu barin gidajensu
  • Tsoron hare-hare ya sa mazauna Rukukuje tserewa zuwa Rijau da Zamfara, yayin da rashin tsaro ke hana manoma zuwa gonaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Wasu manoma biyar sun rasa rayukansu, an sace mutane 18, yayin da ake zargin ’yan bindiga sun kona gidaje da shaguna a wasu al’ummomin jihar Niger.

Hare-haren sun faru ne tsakanin 9 zuwa 12 ga Oktoba, 2026, a al’ummomin Fanga da ke ƙaramar hukumar Mashegu, da Kigbere da Kokani a ƙaramar hukumar Borgu.

Kara karanta wannan

An kai ɗan Najeriya kotu kan ikirarin mallaka da shirin cefanar da jirgin sojoji

Yan bindiga sun yi barna a Neja
Taswirar jihar Neja da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun shiga garin da rana.

Yaushe yan bindiga suka kai hari?

Harin baya-bayan nan ya faru ne a Fanga ranar Litinin, bayan ’yan bindigar sun nemi mazauna yankin su biya miliyoyin nairori a matsayin haraji, amma suka kasa biyan kuɗin.

Mazaunin ya ce ’yan bindigar sun kakaba wa al’ummar haraji sau biyar, amma duk da biyan kuɗin a baya, sun ci gaba da kai musu hare-hare.

Ya ce:

“Sun ƙona ɗaya daga cikin manyan motocinmu, suka shiga shaguna da dama tare da sace kayan abinci. Sun kuma sace mutane 18, ciki har da mata da ƙananan yara. An bar garin Fanga babu kowa.
“Ko da mun biya kuɗin, har yanzu suna dawowa su kai mana hari. A wannan karon, ba mu iya biyan kuɗin da suka nema ba, kuma sun dage cewa idan muna son zaman lafiya, dole ne mu tara kuɗin mu biya."

Kara karanta wannan

Tsaro ya lalace: 'Yan bindiga sun sace kansila da 'ya'yansa 2 a Kaduna

An rasa rayukan a harin yan bindiga a Niger
Gwamna Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Yadda mutane ke tserewa daga gidajensu

Majiyoyi sun ce mazauna al’ummar Rukukuje da ke ƙaramar hukumar Rijau sun tsere daga gidajensu ranar Litinin, bayan samun rahotannin motsin wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a yankin.

Wani mazaunin yankin ya ce wasu daga cikin waɗanda suka tsere sun nufi Rijau, hedikwatar ƙaramar hukumar, yayin da wasu suka tsallaka zuwa jihar Zamfara da ke maƙwabtaka domin neman tsira.

Wani mazaunin ya ce manoma sun tsere bayan an ga wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suna dosar al’ummarsu, cewar Tribune.

Haka kuma, an ga wasu mazauna yankin suna tura babura ta cikin ruwan yayin da suke ƙoƙarin barin al’ummar.

Majiyoyin yankin sun ce rahotannin hijirar waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne sun jefa jama’a cikin fargaba, lamarin da ya tilasta wa iyalai barin gidajensu saboda tsoron yiwuwar kai musu hari.

Yankin Rijau na jihar Niger na fuskantar ƙarin matsalolin tsaro, inda ake zargin ’yan bindiga da ke aiki daga yankunan kan iyaka da Zamfara suna barazana ga mazauna karkara. Zamfara ta shafe shekaru tana fama da matsalar ’yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda ruwan sama ya ruguza allon tallata Tinubu

Dan banga ya harbe wani a Niger

Mun kawo muku cewa akalla mutane uku sun mutu bayan rikici ya barke tsakanin ’yan sa-kai da matasa a Kpakungu da Gbeganu da ke birnin Minna.

Lamarin ya fara ne bayan wani ɗan sa-kai ya harbe wani mutum mai suna Aliyu a yayin wani samame da aka kai Kpakungu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.