Gwamna Ya Sanya Dokar Hana Fita bayan Kona Gidajen Masu Rike da Sarauta

Gwamna Ya Sanya Dokar Hana Fita bayan Kona Gidajen Masu Rike da Sarauta

  • Gwamnatin Bayelsa ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a al’ummar Biseni da ke ƙaramar hukumar Yenagoa
  • An kona wasu gine-gine mallakar sarakunan gargajiya yayin zanga-zangar matasa kan rashin wutar lantarki, hanyoyi masu kyau da sauran abubuwan more rayuwa
  • Gwamna Douye Diri ya umarci jami’an tsaro su dawo da zaman lafiya, yayin da aka ruwaito kama wani matashi bisa zargin taimaka wa wasu wajen tare hanyar shiga kamfanin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bayelsa - Gwamnatin Jihar Bayelsa ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Biseni, da ke ƙaramar hukumar Yenagoa.

Gwamnatin ta sanya dokar ne bayan zanga-zangar tashin hankali da matasa suka gudanar kan rashin ababen more rayuwa a yankin.

An sanya dokar hana fita a Bayelsa
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Rahotan jaridar Daily Trust ya bayyana cewa an ƙona wasu gine-gine mallakar sarakunan gargajiya a yayin zanga-zangar.

Kara karanta wannan

To fa: Gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan sababbin hanyoyin da 'yan ta'adda suka bullo da su

Gwamna Diri ya ba da umarnin hana fita

Gwamna Douye Diri ne ya sanar da dokar hana fita a ranar Juma’a, ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Daniel Alabrah, ya fitar, rahoton The Punch ya nuna hakan.

Gwamnan ya ce an ɗauki matakin ne bayan tabarbarewar doka da oda a yankin. Ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki nan take.

A cewarsa, ya bayar da umarnin ne bayan samun bayanai daga kwamandojin jami’an tsaro kan halin da ake ciki a Biseni.

Ya ce wasu mutane sun tare hanyoyin shiga garin da kuma hanyoyin da ke cikinsa, tare da kunna wuta a kan hanyoyin.

An tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya

Gwamna Diri ya umarci jami’an tsaro da su ɗauki matakan da suka dace domin dawo da doka da oda, zaman lafiya da tsaro a garin.

Haka kuma, ya buƙaci mutanen da ke da kishin zaman lafiya su ci gaba da bin doka, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Biseni.

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yaba wa Sarki Aminu Ado kan muhimmin abin da ya yi

Rashin wutar lantarki da hanyoyi ya jawo zanga-zangar

A halin da ake ciki, rahotanni sun nuna cewa tashin hankali ya ƙaru a Biseni bayan matasa sun gudanar da zanga-zanga kan rashin wutar lantarki, hanyoyi masu kyau da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.

Matasan sun bayyana cewa kamfanin mai da ke gudanar da ayyukansa a yankin ya kamata ya samar da waɗannan abubuwan more rayuwa.

Rahotanni sun ce daga bisani an gudanar da wani taro tsakanin matasan da wakilan wasu ƙungiyoyi, inda aka bayar da tabbacin cewa za a yi la’akari da buƙatunsu.

Sai dai, an ruwaito cewa an kama wani daga cikin matasan bisa zargin cewa shi ne ya ɗauki nauyin wasu matasa wajen tare hanyar shiga kamfanin.

An sanya doka a Bayelsa
Taswirar jihar Bayelsa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An sanya dokar hana fita a Oyo

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Oyo ta sanar da ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10 na jihar.

Gwamnatin ta sanya dokar ne sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankunan da ke makwabtaka da tsohuwar gandun daji ta kasa da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng