Bello Turji Ya Dawo kan Ganiyarsa, Ya 'Ƙarbi' N50m na Haraji daga Talakawa

Bello Turji Ya Dawo kan Ganiyarsa, Ya 'Ƙarbi' N50m na Haraji daga Talakawa

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mazauna garin Yan Buki da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara sun biya Bello Turji da ’yaransa miliyoyin kudade
  • An ce mazauna garin sun biya kuɗin ne domin tabbatar da sakin mutanen da ’yan bindigar suka sace tare da biyan harajin da suka kakaba
  • Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis yayin da al'ummar Zamfara ke ci gaba da fuskantar barazanar ’yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zamfara - Ana zargin mazauna garin Yan Buki da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun bayar da miliyoyin haraji ga Bello Turji.

Rahotanni sun ce mazauna yankin sun biya kusan Naira miliyan 50 ga fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji da yaransa.

Ana fargabar Bello Turji ya karbi na
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Bello Turji. Hoto: Dr Bello Matawalle, HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani rubutu da shafin Bakatsine da ke kawo rahotanni kan matsalolin tsaro ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Mutane 5 'yan gida 1 sun mutu daga kamuwa da cuta a Kano

Dalilin kakabawa mutane harajin N50m

An ce an biya kuɗin ne ranar Laraba domin tabbatar da sakin mazauna garin da aka sace tare da biyan harajin da ake zargin ƙungiyar ’yan bindigar ta kakaba wa al’ummar.

Wani masani kan harkokin tsaro, Bakatsine, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Alhamis, inda bayanan da ake da su suka nuna cewa al’ummar sun biya kuɗin ne domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun nuna cewa an bayar da wannan makudan kuɗaɗe ne a wani yunƙuri na ganin an saki mutanen da ’yan bindigar ke tsare da su, tare da biyan buƙatun kuɗi da ake zargin sun ɗora wa al’ummar.

Wannan lamari ya nuna irin matsin lambar da al’ummomin wasu sassan jihar Zamfara ke fuskanta, inda mazauna yankunan ke fama da satar mutane, buƙatun kuɗin fansa da sauran barazanar aikata laifuka.

Ta'asar da Turji ke yi a yankin Arewacin Najeriya
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Ta'asar da Turji ke yi a yankin Arewa

A cikin ’yan shekarun nan, ana danganta Bello Turji da hare-haren ’yan bindiga, satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci a faɗin Zamfara da yankunan da ke maƙwabtaka da jihar.

Kara karanta wannan

Hukumar fanshon ƴan sanda za ta zuba hannun jari a matatar Dangote

Sunansa ya sha fitowa a rahotannin tsaro da suka shafi ayyukan ’yan bindiga da kakaba haraji kan al’ummomin karkara.

Rahoton biyan naira miliyan 50 ya ƙara bayyana nauyin kuɗaɗen da aka ɗora wa mazauna yankunan yayin da suke ƙoƙarin ganin an saki waɗanda aka sace tare da hana sake kai musu hare-hare.

Al’ummomin wasu sassan Zamfara da sauran yankunan Arewa maso Yamma na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da ƙungiyoyin ’yan bindiga masu ɗauke da makamai ke haddasawa, inda mazauna yankunan ke shiga tsakanin barazanar sace su da buƙatun kuɗi daga masu aikata laifuka.

Ana zargin Turji da sace mutane 40

A baya, mun ba ku labarin cewa akalla mutane 10 ne suka mutu, yayin da aka sace wasu 40 bayan ’yan bindiga da ake zargin mabiyan Bello Turji sun kai hari Tofa.

Wani mazaunin Tofa ya ce maharan sun bude wa jama’a wuta, suka yi garkuwa da mutane tare da sace dabbobi kafin komawa daji.

Yan Tofa da kauyukan da ke makwabtaka da su sun bukaci gwamnati da jami’an tsaro su kara yawan sojoji domin hana sake kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.