Kotun Amurka Za Ta Duba Shari’ar Dan Najeriya da Ya ‘Dafa’ wa Yan Bindiga Abinci
- Kotun Ƙoli ta Amurka ta amince da sauraron ƙarar gwamnati kan neman hana Izuchukwu Ozurumba mafaka a kasar
- Lauyoyin Ozurumba sun ce an tilasta masa aiki a sansanin ’Yan Bindiga, inda ya tsere bayan watanni shida
- Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin farko, amma gwamnatin Donald Trump ta garzaya Kotun Ƙoli, wadda ake sa ran za ta yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Kotun Ƙoli ta Amurka za ta saurari ƙarar neman hana ɗan Najeriya mafaka kan zargin dafa abinci ga ’yan bindiga.
Kotun Ƙoli ta Amurka ta amince da sauraron ƙarar gwamnatin tarayya, wadda ke neman hana Izuchukwu Ozurumba, ɗan Najeriya, samun mafaka a ƙasar.

Source: Twitter
Zargin da ake yi kan Ozurumba a Amurka
An zarge shi da tilasta masa dafa abinci ga wata ƙungiyar ’yan aware da ake kira ’Yan Bindiga, cewar The Guardian.
An ce kotun ta amince ta sake duba hukuncin wata ƙaramar kotu, wadda ta ce aikin Ozurumba na girki bai kai matsayin bayar da “goyon baya na zahiri” ga ƙungiyar ta’addanci ba, bisa dokokin shige da fice na Amurka.
Takardun kotu sun nuna cewa Ozurumba ya tafi wani sansani da ke wani yanki mai nisa a wajen Lagos a shekarar 2022, bayan samun labarin wata damar aiki.
An ɗauke shi aiki a matsayin mai dafa abinci, amma daga baya ya gano cewa ’Yan Bindiga ne ke gudanar da sansanin, ƙungiyar da ake ganin tana da alaƙa da masu fafutukar ballewa a Najeriya.
Lauyoyinsa sun ce ya fara zargin ayyukan ƙungiyar bayan lura da cewa motsin wasu matasa daga sansanin ya yi daidai da rahotannin kashe-kashe da ƙona kadarori.
An ce Ozurumba ya yi ƙoƙarin barin sansanin, amma aka hana shi, aka tilasta masa ci gaba da aiki ba tare da biyan sa kuɗi ba.
Bayan watanni shida, ya tsere a lokacin da aka tura shi sayen kayayyaki, sannan ya koma Lagos.
Lauyoyinsa sun ce daga baya an yi masa duka tare da yi masa barazanar kisa, lamarin da ya tilasta masa tserewa zuwa Venezuela, inda suka ce barazanar ta ci gaba.

Source: Twitter
Yadda Ozurumba ya samu damar shiga Amurka
A watan Yulin 2023, Ozurumba ya shiga Amurka ba bisa ƙa’ida ba ta iyakar kudancin ƙasar, sannan ya nemi mafaka da sauran kariya daga korar sa.
Sai dai, wani alƙalin shige da fice a lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya yanke hukuncin cewa ’Yan Bindiga ƙungiyar ta’addanci ce, kuma aikin Ozurumba na dafa musu abinci ya zama taimaka wa ta’addanci.
Alƙalin ya ce shirya abinci ga mambobin ƙungiyar ya taimaka musu wajen cimma manufofinsu, ta hanyar samar musu da “bukatun rayuwa na yau da kullum”.
Ya kuma yanke hukuncin cewa yanayin aikin Ozurumba, ciki har da ikirarin cewa an tilasta masa zama a sansanin, bai keɓe shi daga dokar hana shige da fice ba, cewar Reuters.
Saboda haka, an ƙi amincewa da buƙatunsa na samun kariya daga korar sa, a shekarar 2025, an mayar da Ozurumba Najeriya, alhali ƙarar da ya ɗaukaka tana nan ba a kammala ta ba.
Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci
A watan Satumban 2025, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Amurka da ke Richmond, Virginia, ta soke fassarar da alƙalin shige da fice ya yi game da ayyukan Ozurumba.
Alƙalai biyu cikin uku na kwamitin kotun ɗaukaka ƙarar sun yanke hukuncin cewa Ozurumba ma’aikaci ne da aka tsare aka tilasta wa aiki, kuma dafa abinci ga ƙungiyar bai zama taimaka wa ta’addanci ba.
Kotun ta ce aikinsa bai samar wa ƙungiyar da wani abu da za ta iya amfani da shi kai tsaye ko karkatar da shi cikin sauƙi domin shirya ko aiwatar da ayyukan ta’addanci ba.
Yan bindiga sun sace manoma 50 zuwa daji
A wani labarin, kun ji cewa ana zargin ’yan bindiga da sace manoma da wasu ma’aikatan gona a Mariga, yayin da shugaban ƙaramar hukumar ya ce adadin waɗanda aka sace ya kai 47.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce masu garkuwa sun tuntubi wasu ’yan uwan waɗanda aka sace, inda suka nemi N2m a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum.
’Yan sandan Niger sun tabbatar da sace sama da mutane 20 a yankin, lamarin da ya haifar da bambanci kan adadin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng


